Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnatin jihar Kano na shirin inganta kudaden shigarta duk shekara da akalla Naira Biliyan daya daga ayyukan hakar ma’adanai a jihar.
Kwamishinan ma’aikatar ma’adanai da albarkatun kasa, Alhaji Safiyanu Hamza Kachako ne ya bayyana hakan a yau a wani shiri na rediyo kai tsaye da daraktan wayar da al’umma na ma’aikatar Adamu Ibrahim Dabo ya saurara kuma ya aikowa kadaura24 .
Alhaji Safiyanu Hamza Kachako ya bayyana cewa tun daga kafa ma’aikatar da Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya Yi, da kuma wa’adin da aka ba ta, ya zuwa yanzu tsare-tsare sun nisa na hada hannu da masu ruwa da tsaki a harkar daga ciki da wajen kasar nan don inganta tattalin arzikin jihar ta fuskanta hadar ma’adainai.
Sabuwar Badakala a Kano: An kama Kantomomi 3 da wasu 19, An kuma Saki Dan Kwankwaso
Kwamishinan ya kara da cewa ma’aikatar karkashin jagorancinsa ta tsara wani shiri na musamman wanda zai inganta kokarin gwamnati na samar da karin ayyuka da guraben aikin yi ga matasanmu masu tarin yawa da kuma kariya ga masu hakar ma’adinai masu lasisi da al’ummomin da ake aikin a inda suke da dai sauransu.

A cewarsa, za a iya cimma hakan ne ta hanyar ci gaba da tantance tasirin muhalli daga ma’aikatar tare da tabbatar da cewa kamfanonin hakar ma’adai suna tallafawa al’ummar da suke aiki a cikin su a duk inda suke a cikin jihar.
Kwamishinan ya kara da cewa a halin yanzu ma’aikatar tana yi lasisin hadar ma’adanai a Gidan Murtala dake birnin Kano.