Gwamnan Abba Gida-gida ya yi alkawarin samar da Karin birane biyu a Kano

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya biya diyyar fulotai ga masu gonakin da aka yanka a kananan hukumomin dawakin kudu da tofa.

Da yake jawabi a yayin raba takardun mallakar fulotan ga masu gonakin da abin ya shafa, gwamna Abba Kabir Yusuf yace an yanka fulotan ne domin rage cunkoso a cikin kwaryar binnin kano da bunkasa yankunan karkara.

“Za mu samar da wasu birane guda biyu domin fadada jihar kano da kuma rage cunkoso a babban birnin jihar”.

Da dumi-dumi: Tinubu ya bayar da umarnin biyan tallafin man fetur – Rahoto

Da yake raba takardun fulotan wanda aka yanka a Rijiyar Gwangwan da Yargaya a karamar hukumar Dawakin Kudu da kuma Unguwar Rimi da Lambu a karamar hukumar Tofa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce samar da fulotan zai bunkasa tattalin arziki da kawo ci gaba a yankin.

Yace an yanka da fulotai 2483 a karamar hukumar Dawakin Kudu yayin da aka yanka 1671 a karamar hukumar Tofa.
Duk da cewa kundin tsarin mulkin kasa ya fayyace cewa dukkanin kasa mallakin gwamnati ce, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa zata biya kaso hamsin cikin dari ga kowanne mai gona domin tabbatar da adalci.

Ya kuma bawa masu gonakin tabbacin gwamnati ba zata waiwayi gonakin da nufin aiwatar da kowane irin gini ba har sai masu gonakin sun girbe abinda suka shuka kasancewar ana cikin yanayin na damuna.

Dawo da tallafin mai: Atiku ya yiwa Tinubu martani mai zafi

A nasa jawabin kwamishinan kasa da tsare-tsare Alhaji Abduljabbar Umar Garko yace wannnan ne karon farko da gwamnati a jihar kano ta baiwa masu gonakin da aka yanka kaso hamsin cikin dari na fulotan da aka yanka a gonakinsu.

Da yake jawabi a madadin masu gonakin da aka yanka, Mal. Sani Abba Rijiyar Gwangwan ya godewa gwamana Abba Kabir Yusuf bisa adalcin da aka yi musu wajen rabon fulotan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...