Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shahararren mai shaguben nan a dandalin sada zumunta Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya bukaci jam’iyyar APC reshen jihar kano da ta janye kalamanta akan shi tare kuma da basu hakuri ko ya ci gaba da yiwa ‘ya’yan jam’iyyar bankade-bankade.
Idan za a iya tunawa Dan Bello ya yi wani bidiyo Inda ya zargi shugaban ƙasa Bola Tinubu da hannu wajen mallakar matatar man fetur a kasar waje da kuma biyan kansu wasu makudan kudade da suna kudin dako da dai sauransu.
Hakan ce tasa mai Magana da yawun jam’iyyar APC na jihar kano Hon. Ahmad S Aruwa ya fito kafafen yada labarai yana musanta labarin na dan Bello tare da cewa akwai bukatar a kama shi domin a tuhume shi kan zargin da ya yiwa shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Abubuwa 10 da suka fito fili sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Faruwar wadancan lamura ne ya fusata Dan Bello Inda a jiya lahadi ya saki wani bidiyo, Inda a cikinsa ya zargi dan takarar mataimakin gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC Hon. Murtala Sule Garo da dibar kudin al’umma tare da sayan wani bangare na guda cikin otel mafi girma a ƙasar saudiyya mai suna Hilton wanda ke daura da masallacin haramin makka.
Wannan bidiyo na Dan Bello ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, Inda wasu suke ganin Dan Bello sharri kawai ya ke yiwa jigon jam’iyyar ta APCn Kano, yayin da a gefe guda kuma wasu suke murna tare da cewa gaskiya ta fara bayyana.
A wannan rana ta litinin da misalin karfe 1 saura Dan Bello ya fito karara ya ce dole ne APCn ta janye kalamanta akan shi, Sannan kuma ta ba shi hakuri tare da Jaafar Jaafar da Bulama bukarti wadanda suma an bukaci a kama su.
“Ya kamata APC Kano ta janye kalamanta da neman afuwa akan zargina da AUDU BULAMA BUKARTI da Jaafar Jaafar akan tayar da tarzoma nan da awa 48. In ba haka ba, za’a shiga NEXT LEVEL.” A cewar Dan Bello
Yadda aka sace Naira biliyan 50 daga asusun Gwamnatin Kano
Kalmar NEXT LEVEL da Dan Bello ya yi amfani da ita yana nufin dai zai cigaba da yiwa jam’iyyar APCn bankade-bankade, musamman Kasancer ita ce ta mika ragamar mulkin jihar kano a hannu jam’iyyar NNPP.
Yanzu dai abun jira shi ne gani ko jam’iyyar zata yi abun da Dan Bello ya bukata ko ko zata dauki wani matakin, muna gefe kuma za mu cigaba da bibiya.