Daga Sani Abdulrazak Darma
Jigo a jam’iyyar LP a jihar Kano Munnir Muhammad Chiranci ya ce za su gudanar a binciken yadda aka boye shinkafar da Gwamnatin tarayya ta kawo jihar kano a rabawa al’umma.
Munnir Muhammad Chiranci, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ‘yan Jaridu a ofishin sa.
“A matsayin mu na wanda su ke tare da al’umma dole ne mu binciki a ina aka ajiye shinkafar, kuma mai ya sa gwamantin jihar Kano bata rabawa Jama’a ba”.
Munnir Chiranci ya kara da cewa tun da gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta turo motocin shinkafa zuwa Jihohin Arewa ciki har da Kano, ya zama wajibi a baiwa mutane, domin ana cikin wahala da yunwa musamman magidanta.
Munnir Muhammad Chiranci wanda tsohon dan takarar a jam’iyyar Labour Party, LP, a Karamar Hukumar Kumbotso, ya ce yanzu haka sun kafa kwamatin bincike a kananan hukumomi 44, domin gano a ina aka boye Shinkafar ta mutanen kano.
Ya bukaci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif da yayi kokarin tallafawa al’umma da Abinchi, da kuma tabbatar da cewa an bayar da Shinkafar da aka Kawo jihar Kano.
Daya juya kan batun halin da ake ciki a Nigeriya Munir Muhammad ya ce akwai bukatar gwamnati ta dawo da Tallafin man fetir da bude iyakokin Nigeriya musammanta Arewa.
Kofa ga Doguwa: Kauce-kauce da zulliya ba za su hana Shari’a ta yi maka kamun kazar-kuku ba
Ya ce mafitar al’ummar Nigeriya su zabi wanda ya ke da kishin kasar, da kawo cigaba da yaki da ‘yan ta’adda, da bunkasa tattakin Arziki, da kuma kula da harkokin noma da kiwo
A karshe ya godewa Malamai da limamai, da suke gudanar da addu’o’i domin samun temakon Ubangiji , akan wahalar da ake ciki, tare da fatan Matasa zasu hakura da zanga zanga, a dage da addu,a.