Doguwa ga Jibrin: Zargin kashe mutane 7 har yanzu yana rataye akanka lokacin da ka kaiwa Kwankwaso, Abba hari a 2019

Date:

 

Kwankwaso, Abba, Madaki manyan shedu ne

Tare da girmama wa ina neman afuwar dukkan dattawa, masu ruwa da tsaki, abokan arziki da ’yan majalisu na Kano da Abuja da ma fadin kasar nan da suka ba ni shawarar in yi watsi da karya, kage, da shirmen da Abdulmumin Jibrin Kofa dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji a jam’iyyar NNPP ya ke yi min.

Ba dan naso ba zan mayar masa da martani na ƙarshe, kan maganganunsa na baya-bayan nan, saboda sun shafi mutuncina da matsayina na ma’aikacin gwamnati kuma ɗan siyasa.

A lokacin da nake jiran Abdulmumini Kofa ya fasa bama-baman da ya yi barazanar idan ya fasa su sai jam’iyya ta ta APC ta koreni, akwai sai na ji Jibrin ya bige da karya, hayaniya da sokiburutsu da shirme.

Kamar yadda kowa ya sani, sa’insar mu ta samu asaline lokacin da Abdulmumini dan ta’addar siyasa kuma dan ta’addar zabe, ya gargade ni da daina sukar “Ubangidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya zagi shugabancin jam’iyyar APC, ya kuma kira mu da Banzaye”, a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu.

Zanga-zanga: Jami’ar SKYLINE ta baiwa Murtala Gwarmai Jakadan Zaman Lafiya

Kamar yadda dattawan Kano da sauran su suka ce na janye daga chachar bakin a kafafen yada labara da muke yi da Jibrin, saboda yaro ne a fagen siyasar kasar nan. Na yarda da ku baki daya, tare da girmama wa, ku yi hakuri, dole ne in mayar da martani kan batun tashe-tashen hankula da rikicin da aka yi a zaben da ya gabata a cibiyar tattara sakamakon zaben mazabar dan majalisar tarayya ta Kano. Shiri ne da makircin siyasa da aka shirya domin dakile nufin Allah (SWT) da fatan al’ummar mazabar T/Wada da Doguwa ta Jihar Kano da suka zabe ni da gagarumin rinjaye. Saboda kaunar da al’umma ta suke yi min take suke min da “ZABE DUBU CI DUBU” Kuma babu shakka a cikin ikon Allah haka abun yake.

Yadda Kotu da yan sanda suka wanke ni:

Tabbas, bisa tsarin shari’armu da kundin tsarin mulki ƙasar mu duk wanda ake tuhuma da wani laifi ba a tabbatar masa da laifin har sai kotun da ta dace ta tabbatar da shi da laifi. A bayyane yake cewa Kotuna har guda uku sun saurari karar nan kuma sun wanke ni, sannan sun bayyana ni a matsayin wanda yake ba mai laifi ba.

Yana da kyau Jibrin da abokansa su sani cewa hukuncin har ma ya umarci gwamnatin jihar Kano da Gwamna da su biya ni Naira miliyan 25 a matsayin diyyar bata min suna da suka yi min ba tare da wani laifi ba.

Kama sojan da ya harbe matashi a Zariya abun a yaba ne — Atiku

Makirci:

Tabbas, akwai rikicin da ya haifar da rigingimun siyasa a yankina, amma ba ni da hannu a cikin rikicin, sai dai abun ma ni ya shafa. Jami’an ‘yan sandan sun kama wasu ‘yan ta’addan da suka yi ikirarin aikata laifin kuma yawancinsu ‘yan jam’iyyar NNPP ne. Wasu ma an dauki hayarsu ne daga cikin birnin Kano domin su je Tudun Wada don hana ni zama dan majalisar wakilai karo na 7.
Kotuna da suke da hurumi a Kano sun yanke hukunci ga ’yan jam’iyyar NNPP da ake tuhuma da aikata laifuka daban-daban.

 

Da girman Allah na gagari duk makiyana na siyasa na cikin gida da na waje, Allah ya tsallakar da ni duk makircin da suka shirya min.

Bari na fito karara na fada cewa a yau dai ni Hon. Alhassan Ado Doguwa, ba wata kotu da nake zuwa gaban a Najeriya, bisa zargin kisan kai, kisan gilla ko duk wani tashin hankali na siyasa da masu zagina ko makiyan siyasa ke yayatawa. Na je gaban yan sanda da kotu sun gudanar da dukkanin wani bincike kan laifuffukan da aka zarge na, amma sun wanke ni akan dukkanin zargin da ake min, kuma takardun da aka wanke ni sunanan a fili ga masu bukatar ganinsu.

Don haka ina so in bayyana karara cewa rikicin da ake cewa ya tashi a yankina, karya ne kuma kirkirar shi akai domin a tade burina na zama kakakin majalisar tarayyar Nigeria. Tabbas burina shi ne na zama kakakin majalisa kuma ba laifi ba ne mutum ya bayyan burinsa na rayuwa. Amma a matsayina na musulmi, a koyaushe ina tuna cewa Allah ne yake ba da mulki ga wanda ya so a sanda ya so…

Zarge-zargen kashe mutane 7 da suka rataye akan Abdulmumini Jibrin Kofa:

Zargin kashe wasu magoya bayan jam’iyyar PDP guda bakwai na nan a rataye a wuyan Abdulmumin Jibrin a lokacin da ya sanya mutanen sa suka kaiwa tawagar magoya bayan Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) wanda a lokacin shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP hari, lokacin da suka je yakin neman zabe karamar hukumar Bebeji a garin Kofa.

Na rantse da Allah ana zargin Jibrin ne ya shirya wannan kazamin harin yayin yakin neman zabe da ya yi sanadin mutuwar mutane. Sanata Kwankwaso ya halarci taron a matsayinsa na jagoran jam’iyyar PDP a jihar Kano a lokacin. Don haka, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma shi ne shaida na kan wannan bakar siyasar da ake zargin Jibrin ya yi a 2019.

Abin takaici, hare-haren da ake zargin sun yi sanadin mutuwar magoya bayan jam’iyyar PDP kusan 7, da wasu da dama da suka jikkata, da kuma kona motoci 25 na magoya bayan Kwankwaso da Jibrin da magoya bayansa suka yi. Hakan ya faru ne a lokacin yakin neman zaben 2019. Allah ne shaidana; Abokina Kwankwaso da daukacin al’ummar Jihar Kano, su ma shaiduna ne kan wannan abin bakin ciki da Jibrin ya yi a yunkurinsa na lashe zaben kananan hukumomi 2, kuma duk da munanan hare-haren da ake zarginsa akai bai yi nasara sai dan takarar PDP da Kwankwaso yayi nasarar lashe zaɓen.

Talla
Talla

Hasali ma, ‘yan sanda sun kama shi tare da wadanda sukai aikin tare har su 70 da aikata laifi. Kuma duk kafafen yada labarai a lokacin sun rawaito kakakin rundunar yan sandan jihar kano na lokacin Abdallahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kuma har ya zuwa yau, ba a gudanar da cikakken bincike kan wannan mummunan kisan gilla da kone-kone ba. Jibrin, kai dan ta’addanci ne, wanda ba ya iya cin zabe kuma dan magudin zabe a siyasar Kano ta yau.

Abokina kwankwaso ya damu sosai kan kisan gillar da Abdulmumini Jibrin ya sa aka yi saboda siyasa. Ina kalubalantar su biyun, in kuma karya ne, Rt. Hon. Ali Madaki, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ta 10, ya musanta hakan.

A kan zarginsa da cewa ina ci zabe ta da karfin tsiya, tambayata ita ce ta yaya na yi na lashe zaben ‘yan majalisar jiha guda biyu na kananan hukumomin Doguwa da Tundun Wada a ranar 18 ga Maris, haka kuma jam’iyyar APC ita ce ta lashe zaben Gwamna a yankina, a lokacin da nake zare a gida bisa umarnin kotu, wanda ya bukace ni da kada in je ko kusa da mazabar tarayya ta?

A karo na goma sha uku, ina kalubalantar Jibrin da ya fito da wadannan bama-bamai da ya ce za su iya sawa a kore daga jam’iyyata ta APC da ba zan taba barinta… A maimakon haka ya kamata ya gabatar da kansa a gaban Sen. Kwankwaso, Gwamna Abba, da Hon. Aliyu Sani Madaki ya sa a kakkabe zargin da ake yi masa da jagorantar wasu gungun ‘yan bangar siyasa wajen kashe mutane a kauyen Kofa a lokacin da suke gudanar da gangamin yakin neman zabe bisa doka a 2019.

Na bar karyar da Kofa yayi al’umma da da yan jaridu su yi nazari kan ta su kuma yanke masa hukunci .

Sa hannu:
Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, OON

Signed:
Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa, OON
* Chairman House of Representatives Committee on Petroleum (Upstream)
* Chairman Northern Regional Caucus of the 10th House of Representatives
* Chairman of House of Representatives special committee on crude oil theft and pipelines vandalisation in Nigeria
* Majority Leader of 9th House of Representatives
*Chief Whip of the 8th House of Representatives
* Former Chairman of the House of Representatives Special Committee on PIB
* Former Chairman of House of Representatives Special Committee on new Naira re-design
*Former Chairman of House Committee on MDGs
August 8, 2024.

8 ga Agusta, 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...