Daga Zakariyya Adam Jigirya
…ya buƙace shi da ya daina saka sunan Tinubu da na Kakakin Majalisa a rigingimunsa
Da alama yaƙin cacar-bakan da ake fafatawa tsakanin Hon Abdulmumin Jibrin Kofa da Hon Alhassan Ado Doguwa, ya sake ɗaukar sabon salo inda Hon Kofa ya sake mayar masa da zazzafan martani. Hon Kofa dai ya tsaya kai da fata sai Doguwa ya nemi afuwa kan yadda yake yawan zagi da yin ƙage ga Jagoran NNPP na kasa kuma Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sannan ya daina zagin ya kuma girmama shi kamar yadda shi Kofa yake girmama shugabannin jam’iyyarsa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta bakin Hadiminsa Kan Yaɗa Labarai, Sani Ibrahim Paki, Hon Kofa ya ce a bayyane take cewa Doguwa bai taɓa lashe halastaccen zaɓe ba a tarihin siyasarsa, sai dai ta hanyar maguɗi da tayar da tarzoma, lamarin da yake jefa mutanen mazaɓarsa cikin halin takaici, hawaye har ma da zargin zubar da jini.
Kofa ya kuma ce a kullum Doguwa na wakiltar mutanensa ne ta ƙarfin tsiya da kuma kama-karya, a samfurin mulkin da za a iya kwatantawa shi da na Idi Amin na ƙasar Uganda.
Ɗan majalisar ya ce kasancewar Doguwa a Majalisar Wakilai har sau bakwai a tsawon shekaru 32 da kuma yadda yake bugun ƙirjin dukkan mukaman da ya riƙe a rayuwarsa a cikin majalisar suke, a daidai lokacin da yanzu haka akwai waɗanda ya kusa yin jikoki da su a majalisar, kamata ya yi a ce shi jam’iyyarsa ta sahalewa ya nemi shugabancin majalisar, kamar yadda ta yi wa wanda ya jagoranci majalisar da ta gabata.
Kama sojan da a harbe matashi a Zariya abun a yaba ne — Atiku
Amma duk da cewar Doguwa ne mutum na farko da ya bayyana buƙatarsa ta neman kujerar tun kimanin shekaru biyu kafin ƙarewar wa’adin wanda ke kai a lokacin, a wani yanayin da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin majalisar, kowa ya san yadda jam’iyyar tasa ta nesanta kanta daga takarar tasa saboda yadda zargin kisan ’yan mazabarsa a lokacin zaɓe ya dabaibaye shi, kuma a yanzu kowa yake jiran ya ga abin da ɓangaren shari’a zai yi a kan lamarin.
“Kazalika, jam’iyyarsa ba ta ga dacewarsa ya zama Mai Tsawatarwa ko Shugaban Masu Rinjaye ba a 2023. Muƙamai biyu muhimmai da ya taɓa rikewa a baya, waɗanda kuma Allah ne shaida, ni na taka muhimmiyar rawa wajen kasancewarsa a kan su, inda na kyautata masa zaton zai canza hali. Amma ina, ya gaza ba mara ɗa kunya,” in ji Hon Kofa.
Ya kara da cewa, “A zahirin gaskiya, duk da dai ya yaƙe mu a lokacin zaɓen Kakakin Majalisa a 2015 da 2019, waɗanda na kayar da shi a duka biyun, ni kaɗai, bisa umarnin Kwankwaso, na tallata shi har aka zaɓe shi Mai Tsawatarwa na majalisar a 2015, sannan na sake yi masa haka a 2019, bayan na jagoranci zaɓen Kakakin Majalisa, inda muka ɗora shi Shugaban Masu Rinjaye bisa umarnin Gwamnan Kano na wancan lokacin, mutane biyun da daga bisani ya ci amanarsu kuma yake ci gaba da yaƙarsu, ko sun sani ko ba su sani ba.
“Doguwa ne cikakken cima-zaunen da ya je Majalisa ba shi da komai, ƙafafunsa sanye da silifas, amma yake ci gaba da zama matsala ga siyasar Kano da ma ta ƙasa baki ɗaya, inda yake kawo rarrabuwar kai tsakanin shugabanni da jama’a kuma yake tunzura jama’a don biyan bukatarsa. Muddin ana son samun zaman lafiya a Kano, sai an yi yi maganin Doguwa, an gane shi da halinsa, a matsayinsa na cikakken maci amana, mai fuska biyu, mai bambaɗanci, mara tausayi kuma maƙaryaci, wanda cikin kusan dukkan maganganunsa 10, guda tara daga ciki ƙarairayi ne tsagwaron su!!!.
Hausawa da malaman addinin musulunci na Kogi sun yi wa Aliko Dangote addu’o’i na musamman
“Ina ƙalubalantar Doguwa da ya nuna mana waye shi a siyasa, ban da kasancewarsa mai amfani da tayar da zaune tsaye, wanda tambarin siyasarsa shi ne raba kan jama’a da haddasa fitina. Muddin bai haɗa mutane rigima ko ya tayar da zaune tsaye ba, ba shi da wani amfani. Ba sai na faɗa ba, ko ina da muƙami ko ba ni da shi, ina da muhimmanci ga al’umma. Amma daidai da rana ɗaya idan Doguwa ya zauna ba shi da muƙami, sai ya shiga matsala. Don haka ba abin mamaki ba ne idan ya bi kowacce irin hanya, ciki har da zargin zubar da jinin mutane, domin buƙatarsa ta siyasa ta biya.
Kantoman Karamar Hukumar Dawakin Tofa ya Kaddamar da Tallafin Abinci ga Mutane 1,610
“Kowa ya san cewa ƙwarewa da gogewata ce ta sa a lokuta daban-daban aka ba ni shugabancin Kwamitin Kuɗi a majalisa, lokacin da shi kuma aka ba shi shugabancin kwamitin da bai kai nawa ba wato na SDGs, sannan ina shugabancin kwamitin kasafin kuɗi lokacin da na yi uwa da makarɓiya ya zama Mai Tsawatarwa, sannan na jagoranci kwamitocin Sufuri da Harkokin Waje da kuma na Gidaje a Majalisar. Ba zan iya ƙirga kwamitocin wucin-gadi da na jagoranta ba, wanda a yanzu shi kuma Doguwa yake hura hanci da wasu ’yan tsirari da ya taɓa jagoranta, bayan tuni duk sa’o’in shi sun yi gaba sun bar shi a wuri ɗaya. Sau biyu ina jagorantar zaɓen shugabannin majalisar da suka yi nasara, kuma na jagoranci Inuwar Sabbin ’Yan Majalisa a 2011 da kungiyar Parliamentary Support Group a 2018. Na fi shi faɗa-a-ji a majalisar, kuma na sha taimaka masa ya samu matsayi a cikinta. Na kai ma a kira ni da sunan ubangidansa a zauren majalisar. Wannan ita ce irin gudunmawar da ƙaramin yaron da yake makaranta a 1992 zai iya ba tsoho irin Doguwa,” in ji Hon Kofa.
Ya kuma ce Doguwa mutum ne da ya tasam ma nitsewa a kogin tarihi, wanda yake neman suna ko ta wanne hali bayan rashin ƙwarewarsa akan shugaban kwamintin harkar mai ta bayyana a idon duniya sannan an toshe duk wata hanya da yake bi ta ganin ido.
Hon Kofa ya kuma gargaɗe shi da ya daina saka sunan Shugaban Ƙasa, Kakakin Majalisa da shugabannin jam’iyyarsa cikin rigingimunsa da kuma ƙoƙarin birge su ta hanyar yin faɗa da mutane da kitsa fitintinu da rarraba kan jama’a a Kano da kuma a ciki da wajen jam’iyyarsa. Har yanzu ba mu manta da surutan da ya yi a zauren majalisa a baya bayan nan ba. Ya zama wajibi ya fuskanci abubuwan da ke gabansa.
“Kamar yadda wani karin magana ke cewa, “Duk tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan doka”, a wannan karon, kamar yadda na yi alkawari, ruwan zai zane wannan tsuntsun saboda na yi alƙawarin tona asirinsa. Ba sa buƙatar shi. Ba za su taɓa so su yi mu’amala da mutumin da ake zargi da hannu dumu-dumu a zubar da jinin mutanensa ba,” kamar yadda Hon Kofa ya ce.