Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Al’ummar Hausawa da malaman addinin Musulunci da ke Jihar Kogi sun hallara a garin Obajana, inda su ka kwashe tsawon sa’o’i uku suna gudanar da addu’o’i na musamman ga shugaba rukunonin kamfanin Ɗangote Alhaji Aliko Dangote, da nufin Allah ya kara bashi rinjaye ya kuma sassauta masa kalubalen da yake fuskanta a harkokin na kasuwanci a halin yanzu.
An fara gudanar da Sallah a Masallacin Umar Tanko da ke Obajana, daga bisani kuma aka yi addu’o’i na musamman ga Dangote, da iyalansa, da kamfanoninsa don Allah ya fitar da kamfanin daga matsalolin da ya kebfuskanta a baya-bayan nan.

Alhaji Idris Dan Iliyasu, Shugaban Kamfanin Satami Global Enterprises kuma wanda ya shirya taron, ya yabawa Dangote, Sannan ya bayyana shi a matsayin mutum mai kima a Najeriya da ma wajenta. Ya jaddada cewa kamfanonin Dangote sun samar da dubunnan ayyukan yi ga matasa tare da bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya.
Iliyasu ya bukaci masu yi wa kamfanonin Dangote zagon kasa da su sake yin la’akari da gudunmawar da yake bayar wajen wajen gina rayuwar al’umma da cigaban tattalin arzikin Nigeria. yana mai cewa illar da ke tattare da yiwa kamfanonin zagon kasa za ta iya shafar ma’aikatanta da iyalansu da ma kasa baki daya.
Sakacin jami’an tsaro ne ya sa masu zanga-zanga su ka yi barna a Kano – Sarki Sanusi II
“Da a ce muna da mutane goma kamar Dangote a Najeriya, da kasar ta zarce matsayin da take a yanzu ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki, idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa”. Inji Dan Iliyasu Satame
A jawabinsa shugaban al’ummar Hausawan Obajana, Mal. Nura Aliyu, ya nuna godiya ga wanda ya shirya taron kuma ya yi addu’ar neman kariya da samun nasara ga Dangote, iyalansa, da kasuwancinsa. Ya kuma bukaci matasan Hausawa da su guji aikata miyagun laifuka, su kuma kai rahoton duk wani abu da basu aminta da shi ba ga hukumomin tsaron yankin.
Taron wanda aka yi saukar karatun kur’ani mai tsarki kusan sau goma, ya samu halartar mutane sama da 500 da suka hada da kungiyoyin addinin musulunci daban-daban.
Matasa sun kwashe shinkafa a tsohon gidan wani jami’in gwamnatin Kano
Idan za a iya tunawa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce wadanda ke cin gajiyar sana’ar shigo da mai ba bisa ka’ida ba, su ne suke kokarin dakile matatar man Dangote.
Obasanjo ya bayyana hakan ne biyo bayan zargin da Shugaban Rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi na cewa wasu wasu mutane na kokarin kawo cikas ga matatar man da ya gina a kimanin Dala Biliyan 20.
Hakan ya zo ne a yayin da aka rawaito cewa har zuwa ranar Litinin matatar man Dangote da sauran matatun mai na gida Nigeria ba a fara sayar musu da danyen man fetur a naira ba kamar yadda shugaba Bola Tinubu ya baiwa kamfanin NNPC umarni.
A wata hira da ya yi da jaridar Financial Times, tsohon shugaban kasar ya bayyana matatar Dangote a matsayin wacce ya kamata a karfafa mata gwiwa don amfanin ‘yan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.