Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnatin jihar kano ta musanta cewa ta kashe naira biliyan 10 wajen siyan kayiyakin Ofis cikin watanni uku na farkon shekara ta 2024.
” Magana ta gaskiya labarin ba gaskiya ba ne, gaskiyar abun da muka kashe shi ne naira miliyan 596, don haka muna kira ga al’ummar jihar Kano da su yi watsi da labarin bashi da tushe ballantana makama”.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Idan za a iya tunawa a ranar laraba, jaridar “Sahara Reporters”, ta rawaito cewa gwamnatin jihar kano ta kashe kimanin naira biliyan 10 wajen siyan kayan ofis.
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya kaddamar da kwamitin mafi karancin albashi
” Ma’aikatar kasafi da tsare-tsare ta jihar kano ta fitar da rahoton yadda aka aiwatar da zangon farko na kasafin kudin jihar na bana a ranar 28 ga watan Yuli, 2024, babu shakka a adadin kudin da suka fitar akwai kuskure, amma ya kamata ayi musu uzuri saboda suma yan adam ne”. Inji Sanusi Bature
Ya ce matakin da gwamnatin Kano ta dauka na fitar da rahoton akan lokaci ya nuna yadda gwamnatin ta ke kokarin yin komai a bayyane ba tare da yin kunbiya-kunbiya ba.
Ya kara da cewa kudaden da aka kashe wajen gyaran da siyan kayan Ofisoshi a wasu daga cikin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar kano bai haura kaso 5 ba cikin 100, amma yace wasu kafafen yada labaran suke ta yada abun da ba haka nan yake ba.
“Ofishin akanta janar na jihar a shirya yake ya bayar da bayanan kudaden da aka kashe a zango farko ga kungiyoyi na ciki da wajen kasar nan.