Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya kaddamar da kwamitin mafi karancin albashi

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamitin ba da shawara kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata na kasa, sa’o’i 48 kacal bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000 kamar yadda suka cimma matsaya da kungiyar kwadago .

Kano ita ce jiha ta farko a fadin kasar nan da ta fara kafa irin wannan kwamiti. An gudanar da bikin kaddamar da kwamitin ne a yau a fadar gwamnatin jihar, wanda mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranta a madadin gwamnan.

A cikin wata sanarwa da ya aikowa kadaura24, Kakakin Mataimakin Gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ya jaddada alhakin kwamitin na tsara yadda ya kamata kan sabon mafi karancin albashin da aka amince da shi da kuma gabatar da shawarwari kan yadda gwamnatin jihar zata aiwatar .

Talla
Talla

Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa aiwatar da sabon mafi karancin albashin zai kara habaka cigaban jihar Kano a dukkanin bangarori, domin jin dadin ma’aikata shi ne abin da gwamnati ta sa gaba.

An dai baiwa kwamitin makonni uku domin ya gabatar da rahotonsa. Gwamnan ya tunatar da ‘yan kwamitin cewa an zabe su bisa cancanta, ya kuma bukace su da su bayar da gamsassun sakamako.

Zanga-zanga: Gwamnatin tarayya ta ba da sanarwa kan gidajen yari

Mambobin kwamitin sun hada da:

– Alh. Usman Bala Muhammad, mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin jiha (Shugaba)

– Alh. Ibrahim Jibril Fagge, Hon. Kwamishinan Kudi

– Alh. Musa Suleman Shanono, Hon. Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi

– Baba Halilu Dantiye, Hon. Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida

– Baffa Sani Gaya

– Prof. Aliyu Isa Aliyu

– Salahudeen Habib Isa

– Ibrahim I. Boyi

– Ibrahim Muhammad Kabara

– Mustapha Nuraddeen Muhammad

– Abdulkadir Abdussalam

– Umar Muhammad Jalo

– Hassan Salisu Kofar Mata

– Yahaya Umar

Talla

Sabon shugaban kwamitin Alh.Usman Bala Muhammad, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin cikin gida ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin jihar bisa amincewar da ta yi wajen zabo yan kwamitin.

Ya ba da tabbacin zasu yi aiki tukuru domin sauke nauyin da gwamnan jihar kano ya dora musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...