Sanata Kwankwaso ya fitar da matsayarsa kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Nigeria

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Jagoran Jam’iyyar NNPP, Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su nemi sauyi ta hanyar dimokradiyya maimakon zanga-zanga.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kan sa kuma aka aikowa kadaura24, ranar Asabar a Kano.

Kwankwaso ya jaddada cewa za a iya samun sauyi mai inganci kuma mai dorewa ta hanyar karfin zabe.

Talla
Talla

Mun tsinci kanmu cikin wahalhalun saboda shugabanninmu sun rasa makama tun a shekarar 2007,” inji Kwankwaso.

“Duk da haka, a ko da yaushe akwai damar yin gyara da dora kasar kan turba mai kyau don bunkasa tattalin arziki, wadata, da kyautata jin dadin ‘yan kasa.”

Gwamnan Kano Ya Kaddamar da Makon Lafiyar Mata da Kananan Yara na 2024

Kwankwaso ya bayyana cewa rikice-rikice da dama a ƙasar sun samo asali ne daga rashin shugabanci nagari, kamar katsalandan da gwamnatin tarayya ta yi a harkokin masarautun jihar Kano, da tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, da rudanin siyasa a jihar Ribas, da rashin tsaro da ya addabi kasar.

Sai kuma rikicin siyasar Jihar Kogi, zagon kasa ga matatar mai ta AIiko Dangote da takaddama game da yarjejeniyar SAMOA.

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun bayyana sharudda ga masu son shiga zanga-zanga a Nigeria

Sauran sun hada da rikicin Sanata Ali Ndume da Shugabancin APC, rashin tsaro da yaduwar miyagun laifuka kadan ne daga cikin rikice-rikicen da za a iya kauce musu.” Inji shi.

Ya kara da cewa wadannan al’amura alamu ne na rashin bin ka’ida da kuma nuna gaskiya.

“Abin bakin ciki ne yadda halayen shugabanninmu na son zuciya da rashin shugabanci nagari ya jefa ‘yan kasa musamman matasa cikin yunwa da rashin tsaro da rashin kyakykyawan tabbas a kasar,” inji shi.

Ya yi kira ga shugabannin Najeriya a dukkan matakai da su magance wadannan kalubale ta hanyar tabbatar da shugabanci nagari da bin doka da oda.

Talla

Kwankwaso ya ce duk da cewa zanga-zanga halak ce a dimokuradiyya, amma yace galibi ta kan kare da tashin hankali, da haddasa asarar rayuka, da barnata dukiya, da kuma tarzoma.

“Ina magana da ku ne ba kawai a matsayina na jagora ba, a’ a ina magana ne a matsayina na ɗan ƙasa, wanda ya imani da cewa ta hanyar zabe ya kamata mu magance matsalolin mu ba zanga-zanga ba.

“Mu sanya kasarmu a gaba, mu hada kai domin gina Najeriyar da dukkanmu muke fatan gani,” a cewar Kwankwaso

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar...

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim   Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin...