Daga Shehu Sulaiman Sharfadi
Majalisar karamar hukumar Dawakin tofa ta jaddada kudirinta na bunkasa sana’o’i domin cigaban mata da matasa a karamar hukumar.
Shugaban riko na karamar hukumar Dawakin tofa Alhaji kabiru Ibrahim Danguguwa ne ya jaddada hakan a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke karamar hukumar.
Danguguwa ya bayyana cewar a kokarinsa na tallafawa matasan yankin domin su dogara da kansu ya sanya an horas da matasa sana’o’in kere-keren motoci a kasuwar kere kere dake kwakwaci a karamar hukumar wanda sanadiyar hakan matasa sama da dubu goma yan karamar hukumar na gudanar da sana’arsu a kasuwar.

Ya kuma bayyana cewar a bangaren ilimi sun samar da cibiyar jarabawar kammala karatun sakandire a makarantar Dawanau, tare da karasa ginin ajujuwa a makarantun dake mazabu goma na karamar hukumar.
Ya kuma bayyana cewar sun sayi scratch card sun rabawa dalibai na makarantun firamare da karamar sakandire ta hanyar zabo hazikan dalibai domin raba musu, sannan ya kuma biyawa daliban yankin dake karatu a Jami’ar Bayero kudin yin rijistireshen na kusan naira miliyan dari da arbain da shida,tare kuma da bada tallafin karatu ga daliban dake karatu a kwalejojin fasaha dana aikin jiyya na kusan naira miliyan uku.
Sanata Kwankwaso ya fitar da matsayarsa kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Nigeria
Kazalika, dangane da sha’anin lafiya, shugaban ya bayyana cewar sun gina asibiti a yankin Dawanau tare da gyara asibitocin karamar hukumar.
Sauran ayyukan sun hadar da gina rijiyoyin burtsatse a fadin karamar hukumar tare kuma da bude cibiyar karatun manya wato yaki da jahilci domin bunkasa ilimi a yankin.
Danguguwa ya baiwa al’ummar yankin tabbacin bujiro da mangartan tsare-tsare da zasu ciyar da karamar hukumar gaba.
Daga karshe ya yabawa gwamnatin Abba kabir yusif bisa kawowa karamar hukumar dauki a kan lokaci.