Daga Maryam adamu Mustapha
Mataimaki na Musamman ga Shugaban Majalisar Dattawa Alhaji Bashir Hayatu Gentile ya Kawo aikin Rijiyoyin Burtsatse guda 19 da kudin su yakai sama da Naira Miliyan 30 a Matsayinsa na hadimin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa.
A ranar lahadin nan ne aka kaddamar da aikin Rijiyoyin Burtsatse a unguwar giginyu dake Karamar Hukumar Nasarawa, Inda aka baiwa Alhaji Rufa’i Dansileka karkashin kamfanin Kabara Enterprises Ltd.
Da yake Zantawa da wakilin Kadaura24 Bashir Gentile yace ya Kawo Rijiyoyin Burtsatse ne domin Magance Matsalolin Ruwa Sha a Jihar Kano, Inda yace aikin na cikin Kasafin kudin Shekara ta 2020. Ya Kuma bada tabbacin cigaba da Kawo irin Waɗanda aiyuka da zasu taimakawa al’ummar Jihar Kano.
Bashir Gentile ya Kuma godewa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan Saboda irin kyautatawa da damammakin da yake basu Matsayin su na hadinman sa.
” Ina godewa Sanata Malam Ibrahim Shekarau Wanda ta sanadiyyarsa na samin Wannan mukamin da har na Sami damar kawo wa al’ummata abun alkhairi, haka zalika dole na yabawa Sanatan Kano ta arewa Sanata Barau Jibril bisa Gudunmawar da ya bayar Wajen tabbatuwar Wannan Aikin kasancewarsa Shugaban Kwamitin Kasafin kudi”. inji Bashir Gentile
Dagacin Garin Giginyu Alhaji Gambo Lawan da Mai unguwa da limamin masallacin Juma’a na giginyu Malam Habib Umar da Sauran al’ummar unguwar ta giginyu na daga cikin Waɗanda Suka hallaci taron kaddamar da aikin Rijiyoyin Burtsatsen.
Yayin kaddamar da aikin, Kamfanin sun da zasu gudanar da aikin sun yi alkawarin kammala aiyukan Cikin Wata guda mai zuwa.
Bashir Gentile ya Kawo aikin Rijiyoyin Burtsatse ne ta karkashin ofishinsa a Matsayinsa na Mataimaki na Musamman ga Shugaban Majalisar Dattawa .