Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kaddamar da aikin dashen itatuwa a hukumance da nufin dasa itatuwa miliyan uku, a kokarin da ake na yaki da sauyin yanayi da kwararrur hamada a jihar .
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, ya ce gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na magance illolin sauyin yanayi, zaizayar kasa, da kwararowar hamada, tare da kara habaka amfanin noma.
“Gangamin dashen itatuwa na shekarar 2024 an yi shi ne domin hana sare itatuwa da kuma dakile illolin sauyin yanayi. Zai kare kasarmu, da bunkasa filayen noma, da yaki da kwararowar hamada,” in ji Gwamna Yusuf.

Jihar Kano na da burin dasa itatuwa miliyan 10 a wa’adin farko na gwamnatin Gwamna Yusuf ta hanyoyi guda uku: jami’an kananan hukumomi, Sarakuna, da magidanta. Sannna za’a rika sanar da yara yan makarantar Firamare da sakandire muhimmancin dashen itatuwa da kuma shigar da ma’aikatan gwamnati, malaman addini, ’yan kasuwa, da masu rike da mukaman siyasa cikin shirin domin inganta yanayin jihar kano.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci sare bishiyu Barkatai ba, inda ya bayyana cewa za a dauki tsauraran matakai kan masu karya doka.
Kungiyar Kwadago Ta Bayyana Matsayarta Kan Zanga-zangar Tsadar Rayuwa a Nigeria
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen gurfanar da duk wanda aka samu yana yankan bishiya ba tare da izinin daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ba,” in ji shi.
“Ina kira ga daukacin mazauna jihar kano da su goyi bayan wannan muhimmin aikin tare da rungumar dabi’ar dashen itatuwa domin amfanin muhallinmu baki daya.
“Bari mu yi aiki tare don kiyaye muhallin mu da tsabta da aminci.”
A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sanusi II, ya bayar da gudunmawarsa wajen gudanar da gangamin, inda ya umurci hakimai da masu unguwanni da su bayar da goyon baya da kuma inganta wannan shiri a yankunansu.
Ya bayyana muhimmancin dashen itatuwa a addini da muhalli, inda ya bayyana muhimmiyar rawar da yake takawa wajen tinkarar kalubalen sauyin yanayi a duniya.
Gwamna Yusuf ya nuna jin dadinsa da irin dimbin goyon bayan da al’ummar Kano suka ba shi, ya kuma bukaci a ci gaba da ba da hadin kai don ganin an samu nasarar wannan aiki da sauran tsare-tsare na gwamnatinsa.