Ba haka mu ka tsammata daga gareku ba – Atiku Abubakar ga majalisar wakilai

Date:

Daga Humaira Abdullah

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya yiwa babbar jam’iyyar adawa a Nigeria takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ce kamata yayi yan majalisar wakilan Nigeria su sadaukar da alawus-alawus din da suke karba ba kashi hamsin din albashin su ba.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito majalisar wakilan Nigeria a jiya alhamis ta ba da sanarwar sadaukar da rabin albashinsu na tsawon watanni shida, domin magance matsalolin tattalin arziki da kasar ta ke fuskanta.

Talla

Alhaji Atiku Abubakar ya kara da cewa tayin da sukai na karbar rabin albashi na tsawon wata shida abun a yaba masu ne amma tayin na su ya gaza a maaunin sadaukarwar da kasar ke bukata a yanzu.

Ya ce akwai alawus-alawus masu yawa da yan majalisun suke karba, wadanda kudade ne masu tarin yawa da ya kamata su sadaukar da su don shawo kan matsalar tattalin arziki da ƙarancin abinchi a ƙasar baki daya.

Dalilan da suka sa NLC ta amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

” Tabbas abun da yan majalisar su ka yi abun yabo ne, amma ba haka ya kamata su yi ba, kamata yayi cikin makudan kudaden da ake basu a matsayin alawus-alawus su ba da rabinsu koma su sadaukar da su duka don kyautata rayuwar al’ummar Nigeria”. Atiku Abubakar

Majalisar wakilci ta dauki matakin don magance tsadar kayan abinchi a Nigeria

“Mun rasa dalilan da suka hana gwamnatin tarayya aiwatar da rahoton kwaskwarima ga hukumumi da maaikatun gwqmnati Oronsaye, wqnda a farkon gwamnatin ta sanr da amincewa da aiwatar da kunshin gyaran kamar yadda gwamnatin shugaba Tinunbu ta shelanta. Mu na ganin yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya suke kashe magudan kudade ba gaira babu dalili, wanda ya kamata ayi amfani da kudin wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar nan ba a rika baiwa wasu shafaffu da mai ba”. A cewar Atiku Abubakar

Alhaji Atiku Abubakar wanda shi ne Waziri Adamawa, ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu tana kashe magudan kudaden da ya kamata ta inganta rayuwar yan Nigeria da su, amma an buge da kashe kudaden ta hanyar da bai dace ba kuma har ana ciwo munanan basussuka wadanda Nigeria bata bukatar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...