Kungiyar AHIP Ta Bukaci Matasa Da Su Nisanci Shan Muggan Kwayoyi Su Nemi Ilimi Da Sana’o’i

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Babbar daraktar kula da harkokin kiwon lafiya da wayar da kan matasa ta ED AHIP Hajiya Mairo Bello ta yi kira ga matasa da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi da dukufa wajen neman Ilimi da sana’o’i domin dogaro da kai.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka aikowa kadaura24 a Kano, domin tunawa da ranar hikimar matasa ta duniya .

Talla

Ta bayyana fataucin miyagun kwayoyi da cin zarafi a matsayin manyan abubuwan da ke haifar da aikata manunan laifuka da sauran abubunwan da basu dace ba a cikin al’umma.

 

Hajiya Mairo ta yi nuni da cewa, ilimi da sana’o’i sune suke inganta rayuwar matasa, har su basu damar zama shugabanni ko rike matsayi a cikin al’umma.

Samoa: Gwamnatin Tinubu na yunkurin danne hakkin yan jarida – Atiku Abubakar

Babbar daraktar ta tabbatar da cewa matasa suna da muhimmiyar rawar da zasu taka wajen cigaban al’umma, musamman idan suka yi amfani da basirar da Allah ya basu ta fannoni daban-daban domin amfanin al’umma.

“Fasahar Sadarwa (ICT), kasuwanci da koyar da sana’o’i ga matasa na da matukar muhimmanci musamman a wannan lokaci da duniyar ta zama a tafin hannu.”

Ta kara da cewa, kasancewar AHIP kungiya ce mai zaman kanta da ta mai da hankali kan matasa, ta horar da dubban matasa sana’o’in dogaro da kai.

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa tsohon Sanatan Kano ta tsakiya mukami

“Za mu iya zama cikin kwanciyar hankali idan muka inganta tunanin mu, muka yi aiki da basirarmu, kuma muka zama masu bin dokoki da ka’idoji .

Taken ranar basirar matasa ta duniya 2024 ita ce “Kwarewar Matasa don Zaman Lafiya da Ci gaba,” da nufin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano da Najeriya baki daya.

Sanarwar ta kuma bukaci gwamnati, masu ruwa da tsaki, da kamfanoni masu zaman kansu da su baiwa matasa fifiko ta hanyar ba su damammaki na don su yi amfani da basirar su ko a magance matsalolin da suka hada da rashin aikin yi da shan muggan kwayoyi a tsakanin Matasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...