Romon Dimokaradiyya: Jobe ya raba Motocin Sama da Naira Miliyan 30 a yankinsa

Date:

  1. Daga Halima M Abubakar
Dan Majalisa mai wakiltar Rimin-Gado, Tofa da Dawakin Tofa zauren Majalisar kasa, Engr.  Tijjani Abdulkadir Jobe ya raba motoci kirar bas guda 10 Wanda kudinsu ya Kai Naira Miliyan talatin domin Waɗanda Suka Sami motocin Suma  su Sha romon dimokuradiyya.
 Da yake jawabi yayin raba motocin  ga wadanda suka ci gajiyar a garin Doka da ke karamar hukumar Tofa a jihar Kano, Jobe ya ce wadanda suka amfana suna da ‘yancin yin amfani da motocin don yin kasuwanci domin su dogaro da kawunansu, inda ya kara da cewa an zabo su ne musamman Saboda gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban mazabun sa.
Yace ya bayar da tallafin motocin ne domin tallafawa Matasan yankinsa su ma su sharbi romon dimokaradiyya ,Sannan yace hakan zai taimakawa Waɗanda Suka Amfana su dogara da kawunansu Sannan Kuma su tallafawa Yan Uwa da abokan arzikin su tare da bunkasa tattalin arzikin yankin.
 Dan majalisar wanda ya samu wakilcin Alhaji Adamu Abubakar Mainasara ya shawarci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su maida hankali wajen tabbatar da kula da ababen hawan domin su dade Suna Amfana, yana mai bada tabbacin cewa a shirye yake ya ci gaba da tallafawa al’ummar da Suka zabo shi.
 Da suke jawabi tun farko, biyu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin Mukhtar Hussain da Naima Yakubu Dan Hakimi, sun godewa Jobe bisa wannan karimcin tare da yin alkawarin yin amfani da ababen hawa yadda ya kamata.

4 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...