Daga Halima Musa Sabaru
Kotun Koli ta Najeriya ta haramta wa gwamnoni rikewa da kuma gudanar da kudaden kananan hukumomin jihohinsu.
Mai Shari’a Emmanuel Agim na Kotun Koli ya kuma ba da umarnin tura wa kananan hukumomi kudadensu kai-tsaye daga asusun Gwamnatin Tarayya.
Ya bayyana cewa ce rike kudaden kananan hukumomi da aka tura daga asusun tarayya da gwamnatocin jihohi suke yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Rikicin Masarautun Kano: Yadda Matasa suka hana wakilin Sarki Sanusi shiga gidan sarkin Rano
Da yake sanar da hukuncin a ranar Alhamis, Mai Shari’a Emmanuel Agim, ya ba da umarnin damka wa kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar kudadensu don su ci gaba da gudanarwa.
Alkalin ya kuma kori buƙatar da gwamnatocin jihohi suka shigar na kalubantar neman hana su tasarrufi da kudaden kananan hukumomin.
Ya bayyana cewa a tsawon lokacin da jihohi suka ki ba wa kananan hukumomi ’yancin tafiyar da kudaden, gwamnatocin jihohin ne ke yin gaban kansu da kudaden.