Mun Rufe Wurin Sallar Da Aka Mayar Da Shi Gidan Gala a Wudil – Bilkisu Indabo

Date:

Daga Samira Hassan

 

Kantomar Karamar Hukumar Wudil, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta ce sun rufe Gidan Gala da ke cikin garin Wudil saboda inganta tarbiyyar al’ummar yankin.

” Dole mu dauki wannan matakin saboda inganta tarbiyyar ya’yan mu, da kuma kaucewa fishin Allah Subhanahu wata’ala”.

Kantomar ta sanar da haka ne a wata ganawa da ta yi da jaridar kadaura24 , inda ta wallafa hotunan yadda ta ziyarci gidan da jami’an tsaro domin tabbatar da rufe shi.

Talla

” Yaran mu na karamar hukumar wudil yara ne da suke zuwa karantar islamiyya kuma suna fahimtar addini don haka bazan bari wasu su zo don su bata musu tarbiyya ba”.

Kotu ta sanya ranar da Ganduje da Matarsa zasu bayyana a gabanta

Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta ce sun je sun rufe gidan galar ne sakamakon rahotanni da suka samu na cewa wurin sallah ne aka mai da shi gidan gala.

” Yau muka gudanar da taron majalisar tsaro ta karamar hukumar kuma daga nan muka tafi da dukkanin jami’an tsaron don gudanar da wannan muhimmin aikin.

Sanata Kawu Sumaila ya gabatar da kudirin kirkirar sabuwar jiha daga Kano

Ta ce a matsayin ta ta mace uwa ba zata zuba ido a rika lalata tarbiyyar yara masu tasowa ba, ” don haka muke sanar da duk wanda yasa aiyukan badala ne suka kawo shi karamar hukumar wudil da ya gaggauta ficewa daga karamar hukumar.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnatin jihar kano karkashin Jagorancin gwamnan Abba Kabir Yusuf ta sha alwashi kawo karshen aiyukan badala a jihar domin kaucewa yada badala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...