Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Majalisar Wakilai ta watsi da yarjejeniar Samoa da Gwamnatin tarayya ta rattaba hannu a kai.
Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar sai an warware duk sarkakiyar da ke tattare da ita.
Majalisar ta cimma wannan matsaa ne a ranar talata, sakamakon dambarwar da ta dabaibaye yarjejeniyar.

Idan za a iya tunawa jaridun Nigeria sun rawaito cewa gwamnatin tarayya ta rattaba hannu akan yarjejeniyar Samoa, wadda ake zargin akwai batun ba da dama ga masu rajin kare hakkin masu auren jinsi su ci karen su babu babbaka.
Mun fito da sabon Tsaro Hana aiyukan laifi a karamar hukumar Gezawa – Kwamandan yan sintiri
Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta cewa akwai batun auren jinsi a cikin yarjejeniyar.