Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta Jihar Kano, Murtala Sule Garo ya karbi Lambar girmamawa daga Kungiyar Ma’aikatan albarkatun Fetur da Iskar Gas ta Najeriya Wato Pengassan.
Shugaban Kungiyar reshen DPR Mr. Owan Abua yace sun Karramawar Kwamishinan ne Saboda irin Gudunmawar da yake bayarwa ta fuskar Siyasa da tattalin arzikin al’umma tun daga tushe.
Kwamishinan wanda ya sami wakilcin Daraktan duba aiyuka na ma’aikatar ƙananan Hukumomin, Salisu Dan’azumi Tahir, yace kwamishinan ya sadaukar da lambar yabon ga Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mutanen Kano.
Murtala sule Garo yana mai cewar Gwamnan da al’ummar Kano sun cancanci yabo saboda irin hadin Kan da suke bashi a matsayin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu karo na biyu .
Alh. Murtala Sule Garo ya ba da tabbacin zai ci gaba da gudanar da ingantattun ayyuka ga jama’a don tabbatar da ci gaba Mai dorewa a Ma’aikatar da kuma jihar Kano baki ɗaya.
Ya Kuma godewa Kungiyar ta PENGASSAN saboda karramawar da suka yi masa, sannan ya yi fatan cewa tanade -tanaden Dokar Masana’antu zai kawo canje -canje na musamman ga masana’antar mai da iskar gas.