Gwamna Yahaya Bello: Shugaban da ya dace ya jagoranci Najeriya zuwa Tudun Mun tsira

Date:

Daga Khadija Abdullahi Umar
 An haifi Alhaji Yahaya Bello ranar 18 ga Yuni, 1975 a Okene, Jihar Kogi, Shi ne ƙarami a cikin ‘ya’ya shida da Mahaifinsu ya haifa.
 Yahaya Bello ya halarci Makarantar Firamare ta Agassa dake karamar hukumar Okene a Shekarar1984.
 A lokacin yana firamare Yahaya Bello an nada shi a Shugaban ajin su (Monitor) bayan ya shiga aji shida aka bashi mukamin Shugaban ɗalibai na makarantar (Head boys).
 Yahaya Bello Ya halarci makarantar sakandare ta Agassa, Anyava, Agassa-Okene Inda ya kammala Karamar sakandare (JSSCE) da kuma babbar sakandare (SSCE) a Makarantar Sakandaren Gwamnati, Suleja-Niger State a 1994.
 Daga nan ya halarci Kwalejin fasaha ta Zaria dake Jihar kaduna a Shekarar 1995 daga nan ya ya Yi digirinsa na ilimin akanta a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a Shekarar1999.
 Yahaya Bello ya yi digirinsa na biyua Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya karanci harkokin gudanar da Kasuwanci a 2002.
 Alhaji Yahaya Bello ya zama cikakken Mamba a Kungiyar Akantoci ta Najeriya a 2004.
 Sha’awarsa na hidimtawa Al’ummarsa, Jiharsa da Ƙasa biki daya, hakan tasa Yahaya Bello ya shiga harkar siyasa, don Al’ummarsa su amfana da Arziki, Kwarewa da gogewar da yake da su.
 Yahaya Bello mai son zaman lafiya ya yi takarar kujerar gwamnan jihar Kogi a 2015, Kuma an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kogi na 2015 bayan da aka zabe shi a kan jam’iyyar A PC a matsayin wanda zai maye gurbin marigayi Abubakar Audu wanda da farko ya lashe zaben. Prince Audu ya rasu kafin a bayyana sakamakon zaben.
 A ranar 16 ga Nuwamba 2019, al’ummar jihar kogi sake zaben Bello a wa’adi na biyu bayan ya doke dan takarar PDP Musa Wada da kuri’u sama da 200,000.
 Gwamna Yahaya Bello shi ne zakaran gwajin dafi Cikin gwamnonin da aka taba yi a jihar Kogi Saboda aiyukan cigaban al’umma dana raya Kasa daya gudanar a Jihar Musamman a fannin Ilimi, Kiwon lafiya, ababen more rayuwa, tallafawa matasa, Noma, Kimiyya da Fasaha, Kasuwanci da masana’antu, yawon buɗe ido da dai Sauransu .
 Kasancewarsa mai son zaman lafiya kuma matashi mai kishin ƙasa mai cike da hangen nesa da hazaƙar Shugabanci, Ƙungiyoyi da dama a Ƙasar nan suna ta kira ga Dan kishin Kasa Alhaji Yahaya Bello da ya fito takarar Shugabancin Najeriya.
 Wadancan Matasa Sun yi imanin cewa Wannan ne lokaci Mafi dacewa da ya kamata a baiwa Matasan Najeriya damar nuna Kwarewa da hazaka wajen jagorantar Kasar nan domin kaita Tudun mun tsira.
 Lallai Najeriya na buƙatar Mutum kamar Gwamna Yahaya Bello da zai shugabanceta a Shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...