Yan Jarida Sun Nemi Masu Hannu Da Shuni Su Yi Koyi Da Farfesa Abubakar Gwarz
Kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Jihar Kano dake karkashin kungiyar ‘yan jarida ta kasa, wato NUJ ta yabawa wanda ya kafa kuma Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kafa Jami’ar a nan Kano.
Shugaban kungiyar, Ibrahim Garba Shuaibu ne ya yi wannan yabon lokacin da wani jami’in Jami’ar, Alhaji Aliyu Kakaki ya jagoranci membobin kungiyar suka zagaya Cikin Jami’ar .
Ya bayyana cewa kafa Jami’ar Maryam Abacha American University a Kano zai kawo ci gaba ta fuskacin haɓbaka Ilimi, zamantakewa da tattalin arziƙin al’ummar jihar Kano da Kasa baki daya.
Ya ce, “Mutanen Kano musamman ‘yan kasuwa, za su ci gaba da yaba irin gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban garin.
Ya bayyana gamsuwa da yanayin kayayyakin fasahar da aka sanya a Jami’ar.
Shugaban ya yi amfani da damar wajen godewa Farfesa Gwarzo saboda tallafin da ya ke bai wa matasa da talakawa da sauran masu rauni a jihar nan ta hanyar Gidauniyarsa ta Adamu Abubakar Gwarzo Foundation (AAG).
A Saboda haka, ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni a jihar Kano da su yi koyi da Farfesa Gwarzo ta hanyar kafa irin wannan Jami’ar domin haɓbaka ilimi a jihar.
An zagaya da membobin kungiyar wasu wurare a cikin Jami’ar da ya hada da ginin Hukumar Gudanarwa, ajujuwan karatu, dakunan gwaje-gwaje, gidajen ma’aikata, dakunan kwanan dalibai da dakin karatu da dai sauransu.