Ganganci ne aikata Laifuka a unguwar Hotoro — Muntari faris

Date:

 

Daga Sani Magaji Garko

 

Kungiyar tsaro da kare dukiyoyin al’umma ta Vijilantee ta ce ganganci ne tunanin aikata lefuka a Unguwar Hotoro da ma karamar hukumar Nasarawa ba ki daya.

Matemakin kwamandan Kungiyar na karamar hukumar Nasarawa Muntari Faris Hotoro ne ya bayyana hakan cikin dare lokacin da suka kama rukunin biyu na mutane daban-daban wadanda suka dauki mata a Mota tare da kaisu yankin Unguwar ta Hotoro domin yin lalata.

Muntari Faris ya ce kungiyar zata sa kafar Wanda daya da duk wani mutum da ya ke kokarin aikata lefuka a Hotoro da Nasarawa da ma jihar Kano ba ki daya.

Ya ce rukunin mutanen biyu dukkan su an kama su ne a tsohon filin Lazio Wanda yanzu ake gine-gine a yanzu a cikin sa sun labe a cikin motocin su suna aikata ayyukan da basu da ce ba, inda ya ce tuni suka Mika su ga hukumar Hisbah ta karamar hukumar Nasarawa domin fadada bincike tare da daukar mataki na gaba, ya na Mai cewa zasu bibiyi maganar har ya zuwa karshen ta.

“Mutum na farko da muka kama mun same shi Yana cikin mota me tinted, har ya kwabe wandon sa don wandon ma Yana hanun mu a haka muka tafi dashi ofis. Muna kokarin kammala wannan sai ga wani can gabar da mu a cikin mota kirar peagueu maza biyu da ma ce daya, dayan Yana waje akan motar yana danna waya, shi Kuma dayan suna cikin motar tare da macen suka aikata ashsha, hakan ya sa muka fara kama su saboda su sun ma fi na farkon kwarewa da zafin Kai, Amma dukka mun kama su mun Mika su hanun DC na Hisba na Nasarawa”.

 

“Na farkon da muka kama ya ce matar sa ce Amma bincike shi zai tabbatar da hakan, Amma ko da matarsa ce Dan me zai tawo da ita titi domin ya gana da ita. Shi wancan tantirai ne Kuma dukka zamu dauki mataki daga Hisba har zuwa kotu”.

Muntari Faris daga nan ya ja kunnen masu aikata irin wannan lafi da su guji hakan musamman a Unguwar Hotoro inda ya ce aikata hakan ga bako kuskure ne Amma da Dan unguwa ko yankin ganganci ne domin duk Wanda ya ke a Karamar hukumar Nasarawa da ma Kano ya san cewa Hotoron Arewa ba guraren aikata ire-iren wadannan lefuka ba ne.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...