Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin wata katafariyar gada a kofar Dan’agundi dake cikin birnin Kano, wadda zata lakume kudi Naira biliyan 15.
Gwamnan wanda ya kaddamar da aikin ranar Lahadin ya ce gwamnatin sa zata gudanar da aikin ne don rage cunkoson ababen hawa,sannan kuma ya mayar da birnin zuwa matsayin babban birni.
Idan zaku iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Gwamna Yusuf a watan Disamba, 2023, ya ba kamfanin CCG Nigeria Limited aikin na biliyoyin nairori tare da bukatar su kammala aikin cikin watanni goma sha takwas.
Hasashen yanayin da zai kasance Yau Litinin a Birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
An bayar da wannan aiki ne tare da aikin wata gadar a Tal’udu dake tsakiyar birnin kano, don sauƙaƙe cunkoson ababen hawa.
“Mun kirkiro hanyoyin da za a iya amfani da su kuma ana sa ran masu ababen hawa za su bi ka’idoji don kare lafiya tare da ba da damar gudanar da aikin yadda ya kamata.”
Abubuwan da ya kamata yan Arewa su yi don amfana da mulkin Tinubu – Kwankwaso
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya aikowa kadaura24 , ya ce samar da ababen more rayuwa wani yanki ne mai matukar muhimmanci a wannan gwamnati inda gwamna Yusuf ke ware dimbin kudade don ciyar da Kano gaba.