Kotu ta sanya ranar fara sauraron Shari’ar Ganduje kan korar shi daga APC

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

Wata babbar kotun jihar Kano ta sanya ranar 27 ga watan Mayu, 2024, domin fara sauraron kararraki guda uku kan dambarwar dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

 

Mai shari’a Usman Malam Na’abba ne ya jagoranci zaman kotun bayan sauraron lauyoyin ɓangarorin biyu, sun sanya ranar da za a ci gaba da sauraren karar.

Da dumi-dumi: NNPC ya sanar da ranar da Zai kawo karshen ƙarancin man fetur a Nigeria

Masu shigar da karar, sun haɗa da: Haladu Gwanjo da Laminu Sani Barguma ta hannun lauyansu, Ibrahim Abdullahi Sa’ad sun shigar da kara mai lamba 13 a ranar 16 ga Afrilu wanda mai bukata na biyu ya goyi bayansu.

Sojoji sun tarwatsa maɓoyar ƴanbindiga, sun kuɓutar da mutane a Taraba

Bayan sauraren bukatun masu shigar da karar tare da yin tambayoyi wanda aka ƙi yarda a amsa a farko, bukatun masu karar na haɗin gwiwa ne da ƙalubalantar hurumin kotun na sauraron karar .

Wanda suka shigar da karar na neman kotu ta yanke hukuncin dakatar da Abdullahi Umar Ganduje na wucin gadi.

Yanzu dai alƙalin kotun ya sanya ranar 27 ga watan mayu na wannan shekarar domin fara sauraren Shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...