Daga Mubina Mahmoud
Kungiyoyin ‘yan jaridu dake a fitaccen gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV) Kano, sun nemi gwamnatin jihar Kano ta shiga tsakani sakamakon barazanar da Manajan Daraktan gidan talabijin Mustapha Adamu Indabawa ya ke yi musu.
Matsalar ta samo asalin ne daga lokaci da kungiyoyin uku na kungiyar yan jaridu reshen ARTV NUJ d kungiyar ma’aikatan Radio Talabijin da wasan kwaiwayo RATTAWU da kuma kungiyar mata yan jaridu NAWOJ suka fuskanci aiki ya fara lalacewa a gidan talabijin din saboda rashin kayan aiki da kuma iya shugabancin, hakan tasa suka zauna a tsakanin su tare da daukar wata matsaya da suka kudir aniyar sanar da shugaban gidan talabijin din.
Lokacin da kungiyoyin suka zauna da shi Manajan daraktan sun sanar da shi mawuyacin halin da gidan talabijin din yake ciki tare da bashi shawarwarin yadda za’a magance matsalolin.
Yadda akai Rarara ya yi min waƙa – Fatima Mai Zogale
Sai dai Maimakon ya duba batutuwan da suka kawo masa, sai (Indabawa) ya hada kai da shugaban ma’aikata (SO) na tashar Ibrahim Bello domin, Inda suka fara yin barazana ga shugabannin Kungiyoyi guda uku.farauta,
An yi zargin cewa shugaban ma’aikatan ARTV din ya haura sama da shekaru goma a gidan Wanda kuma hakan ya sabawa ka’ida.
Wata majiya mai tushe daga gidan talabijin din ta shaidawa KADAURA24 cewa tuni manajan daraktan ya bukaci shugaban ma’aikatan da ya kundin bayanai (fales) na shugabannin Kungiyoyi uku domin fitar da su daga tashar.
Majiyar ta ce duk da cewa gidan talabijin na ARTV ya samu kusan naira miliyan casa’in (90) na kudade daga shirin Majalisar Dinkin Duniya na ARID, yana fama da rashin isassun kayan aiki, lamarin da ke tilasta wa ma’aikatan aron kayan aikin domin gudanar da aiyukan su .
Haka kuma wata majiya ta shaidawa mana cewa MD ya dorawa wani kaninsa mai suna Auwalu Manajan akan wasu ayyuka na tashar, wanda hakan ke kama da sanya yan uwa cikin aiyukan gwamnati, kuma ana zargin Auwalu Manajan da yin barazana ga duk ma’aikacin da bayan bin akidarsu.
Majiyar ta kuma bayyana wa wannan Jarida cewa, kanin MD ana zargin sa da karkatar da man dizal din da aka tanada domin gudanar da aikin gidan talabijin din zuwa wani wuri na daban kuma duk hakan na faruwa da sanin MD.
Hukumar NEMA ta Bayyana Adadin Wadanda Suka Rasu a Hatsarin Ginin da Afkawa wasu a Kano
Ana kuma tuhumi Auwalu Manaja da yin abubunwan da basu dace ba a wasu daga cikin gine-ginen tashar, inda ake zargi maza na kawo Mata domin aikata masha’a.
An kuma tattaro cewa, a baya-bayan nan, dan uwan MD ya dauki hayar wasu bata gari inda suka shiga har cikin tashar don kai hari tare da kashe daya daga cikin abokansa sakamakon rashin fahimtar juna a tsakaninsu.
Har ila yau, kadaura24 ta sami labari yadda Ake zargin shugaban gidan talabijin din na ARTV da yin sama da fadin wata taliya katan 300 da aka Kai gidan domin tallafawa ma’aikatan ARTV a lokacin azumin watan Ramadana.tuna yadda.
Haka kuma, an gano cewa Mustapha da shugaban ma’aikatan ARTV Ibrahim Bello sun shirya sayar da rukunin gidajen ma’aikatan gidan talabijin na ARTV da ke kan hanyar Sabo Bakin-zero a karamar hukumar Nassarawa.
Global Tracker ta tuntubi manajan darakta na Alhaji Mustapha Indabawa wanda ya musanta dukkan zarge-zargen, inda ya kara da cewa shi ma yana farautar kalubale daga wasu mutane a tashar.
Babu wata barazana da ake yiwa yaya ya’ya ko shugabannin Kungiyoyi NUJ, RATTAWU, ko NAWOJ, inda ya kara da cewa shugabannin NAWOJ sun bayyana masa sarai cewa ba za su shiga duk wani yunkuri na yi masa bara’a ba .
“Lokacin da na karbi mukamin MD, gidan talabijin din nan karfe 04:00 yamma yake fara Aiki na zuwa karfe 12:00 na dare, ita kuma radiyon dama bata aiki kwata-kwata, amma kamar yadda nake magana da kai yanzu gidan Talabijin yana fara aiki daga karfe 08:00 na safe kuma an rufe 12 na dare. ” Inji Mustapha.
Sanarwa ta Musamman Daga Hukumar Samar da Ruwan sha ta Jihar Kano
Manajan ya kuma karyata jita-jitar da ake yadawa cewa yana shirin sayar da gidajen aikin na ARTV, Inda ya ce yana kalubalantar duk wanda yake da hujja da ya gabatar da ita.
Dangane da batun Auwal Manaja kuwa, MD ya bayyana cewa ya fadawa masu ruwa da tsakin tashar cewa ka da kowa yayi aiki da Auwalu Manajan hukumance saboda ba ma’aikaci ba ne , yace ya fada musu duk Wanda ya ki kuma to shi babu ruwansa a ciki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a ranar Juma’a sun jami’an hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano sun kwashe sama da sa’o’i uku suna gudanar da bincike a gidan.
Mun kuma tuntubi Auwalu Manajan wanda ya ki cewa komai kan lamarin