Jihohin Nigeria na koyi da Kano Wajen Samar da Magunguna – Dr. Tsanyawa

Date:

Daga Halima M Abubakar
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ziyarci wurin adana magunguna na jihar Kaduna.
Wannan na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Jami’a hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano Hadiza M Namadi ta aikowa Kadaura24.
 Dokta Tsanyawa ya bayyana cewa ziyarar Wani kokari ne na kyautata dangantakar Aiki tsakanin su, Kamar yadda Shugabanin Hukumar kula da magunguna ta Jihar kaduna suka ziyarci Kano don koyon yadda Aikin Shirin asusun Samar da magunguna yake gudana da yadda ake gudanar da shi.
 Sanarwar tace kwamishinan ya kara da cewa jihar Kano ta zamo zakara a Cikin takwarorinta jihohin Kasar nan Saboda yadda Hukumar kula da magunguna ta Jihar Kano take gudanar da Shirin yadda ya kamata.
 Dokta Tsanyawa ya kuma bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yana ba da cikakken goyon baya ga shirin Asusun Samar da magunguna a jihar wanda shine dalilin da ya sa jihar Kano ke ɗaukar nauyin shirin DRF a Najeriya a matsayin cibiyar Shirin a Kasar nan.
 Daga karshe ya ce Gwamnan Kano koyaushe yana jajircewa tare da saka jari mai yawa a fannonin kiwon lafiya domin inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Yayin Ziyarar Kwamishina Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa na tare da Babban Darakta na Hukumar kula da Magunguna ta Jihar Kano Pharm. Hisham Imamudden.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ga Duniya baki daya – Shugaban kamfanin Yahuza Suya

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Shugaban kamfanin Yahuza Suya & Catering...