Adam A Zango ya yi suka mai zafi tare da zargin yan masana’antar Kannywood kan halin da yake ciki

Date:

Daga Hafsat Lawan Sheka

 

Jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana cewa masana’antar tasu cike take da yan bakin ciki da mahassada da kuma maciya Amana.

 

“Akwai mutanen da yawa dana taimakesu wasu kuma nine sanadin ɗaukakarsu, amma su na gani ana zagina basa iya kare ni, duk da sun san cewa abinda ake zaginna akansa ba gaskiya bane, ba hali na bane “. Inji zango

 

Zango ya bayyana haka ne cikin wani fefen bidiyo da ya saki a ranar Lahadi, inda yace mutane irinsu, Falalu Dorayi, Ado Gwanja, Abubakar Sani, Zainab Indomie da sauransu, duk ya taimakesu wasu ma har kyautar mota ya basu, shi yasa yake jin tsoro akan abinda ya faru da Marigayi Rabilu Musa Ibro da Aminu S Bono, a lokacin da suke raye da kuma bayan rasuwarsu.

EFCC ta yi Martani game da labarin wanke Ministar Jin kai Bette Edu

Cikin jawabinsa, Zango ya buga misali da Darakta Ashiru Nagoma da kuma tsohon jarumi Bashir Bala Chiroki, wanda yace duk laifin da suka aikata a Kannywood ya kamata a yafe musu, a taimakesu domin sun iya kuma sun bada gudummawa a masana’antar, kuma Allah ma ana yi masa laifi a nemi afuwarsa kuma ya yafe ballantana Kannywood.

Adam A Zango ya Bayyana Dalilan da Suka sa ya Daina Fitowa a Fina-Finan Kannywood

A batun zamantakewar aure tsakaninsa da iyalinsa, Zango yace a cikin matan da yayi zaman aure dasu bai fi guda biyu ne suka yi rabuwa bisa wasu dalilai marasa ƙarfi ko kuruciya ba, amma ragowar duk sun aikata masa wasu laifuka da idan ya bayyana su sai an jinjina masa.

Mai Yan masana’antar kannywood din suka ce

Wasu daga Cikin yan masana’antar sun Magantu Kan bayanin na Adam A zango, Inda wasu suka ga laifinsa wasu kuma suka bayyana goyon baya kan abubunwan da ya fada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...