‘Yan sanda sun kama mutane 54 da ake zargi da shirin Tada Tarzoma a “Hawan Daushe” a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 54 da ake zargi da yunkurin kawo cikas ga Hauwan Daushe a sassa daban-daban na jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ne ya bayyana haka a wata wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa kadaura24 ranar Alhamis.

“Mun kama mutane 54 dauke da muggan makamai daban-daban da Ake zargin suna shirin kawo cikas ne ga bukukuwan Sallah da ke gudana a sassan jihar.

Sallah: Ku Cigaba da Yiwa Nigeria addu’o’iin Samun Cigaba – Minista Gwarzo

Kayan halaifin da aka kwato a wajen matasan sun hada da wiwi, babura da wasu muggan makamai da dai sauransu.

“Mun samu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu matasa suna ta taruwa a cikin sirri wadanda suke so su nuna cewa su masoyan wasu manyan masu mukaman siyasa ne a jihar Kano.

“Sun shirya kai ta da hatsaniya a harabar filin Hawan daushe wanda Masarautar Kano ta saba shiryawa .

” Matakin akwai yuwuwar ya jawo martani daga abokan burminsu da zai haifar da karya doka da oda a jihar.

Hotunan Yadda Sarkin Kano ya gudanar da Hawan Sallah

Hawan daushe ba wajen siyasa ba, kuma duk wani nau’i na nuna alamun jam’iyyun siyasa, sanya T-shirts, ko hula, ko daga allunan yan siyasa abu ne da ya karya doka kuma ba zamu lamunta ba.

Rundunar yan sandan ta shawarci ‘yan siyasa da su yi kira ga magoya bayansu da su guji yin duk wani abun da zai haifar da tsarzoma a bikin sallah na al’ada da aka saba.

Ya ce wadanda ake zargin da suka zo cin gajiyar ranar farko ta Sallah an kwashe su daga titunan masarautu biyar na jihar Kano.

“Babu sarari ga masu aikata laifuka saboda haka ‘yan sanda suna gargadin masu kunnen kunne da su saurara yayin da ake kara kai hare-hare kan wuraren da aka gano masu aikata laifuka,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Karamin Ministan gidajen da raya burane...

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...