Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Rahotanni daga Kasar Saudiyya na nuni da cewa tuni hukumar kula da duban wata ta Kasar ta fita tare da ba baza jami’an ta domin fara duban watan a wannan rana ta litinin.
Yanzu-yanzu: CBN Ya Sake Karya Farashin Dala a Nigeria
KADAURA24 ta ruwaito Jami’an sun girke kayan aikin wadanda da suka haɗar da na’urori na zamani domin su gudanar da aikin na su yadda ya kamata.
Sai dai masana ilimin taurari a Kasar sun cewa zai yi yuwa a ga jinjirin watan na Shawwal na shekara ta 1445.
Majalisar Dokokin Edo Ta Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da shafin Haramain na internet ya fitar a wannan rana.
“Galibin masana ilmin taurari sun yarda cewa zai yi wahala a iya ganin jaririn watan Shawwal 1445 a yau, amma a cikin ‘yan kwanakin nan Sudair Observatory ta tabbatar da cewa sun yi kuskure a lokuta da dama”.
Sai dai wannan bayanin bai dakatar da jami’an duban watan daga aikin su na cigaba da neman jinjirin watan na Shawwal ba.
Sai dai rahotannin da suke iske mu yanzu haka da misalin karfe 3 saura a gogon kasar, yanayin hadari da gajimare ake fuskanta a yankin Riyadh da Tumair da Sudair dake kasar ta Saudiyya.