Daga Hafsat Lawan Sheka
Dan majalisar dokokin jihar Kano, Alhaji Halilu Ibrahim Kundila ya rasu.
Halilu Kundila, wanda shi ne dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Shanono/Bagwai, ya rasu da yammacin ranar Asabar.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa SOLACEBASE cewa dan majalisar da ya raba kayan tallafin azumi ga al’ummar mazabarsa a makon jiya ya rasu ne a gidansa da yammacin ranar Asabar da ta gabata.
Ganduje ya yi martani kan gwamnatin Kano bisa gurfanar da shi a gaban Kotu
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana’izar Alhaji Halilu Ibrahim Kundila dan jam’iyyar APC mai shekaru 59 a duniya a safiyar Lahadi a Kundila da ke karamar hukumar Shanono ta jihar Kano.
Daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar akwai dan majalisar wakilai mai wakiltar Shanono/Bagwai a zauren majalisar tarayya Hon. Yusuf Ahmad Badau.
Marigayin dan majalisar mai shekaru 59, ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 17.