Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Biyo bayan korafe-korafen da al’umma keyi a kan shirya fina-finan dake nuna fadan Daba da harkar Daudu a jahar Kano. Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano Abba El-mustapha ya bada umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan dake nuna fadan daba da harkar daudu a fadin jahar Kano.
Abba El-mustapha na bada wannan umarni ne a yau jim kadan bayan wata ganawa da yayi da manyan ma’aikatan Hukumar tace fina-finan na Kano tare da wasu daga cikin wakilan yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood wanda suka hada da kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS DIRECTORS da kuma PRODUCERS.
Jami’an Tsaro sun kwaci masu Garkuwa da mutane a hannun Matasa a Kano
Abba ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin yaci karo da tarbiya tare da al’adar al’ummar dake jahar, a saboda haka tuni lokaci ya shige da za’a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su cigaba da yaduwa a cikin al’umma.
Abba El-mustapha ya godewa yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood dangane da hadin Kai da kuma goyan bayan da suke bawa Hukumar a koda yaushe.
Gwamnatin Nigeria ta bayyana wadanda karin wutar lantar ya shafa
A karshe ya kara godewa al’ummar jahar Kano kan irin hadin kan da suke bawa Hukumar musamman na sanar da ita duk wani abu da suke ganin ya saba da al’ada tare da tarbiyar addinin musulunci.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar tace Fina-Finai Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, yace Abba El-mustapha ya kuma yi alkawarin cigaba da barin kofar sa a bude domin karbar shawarwari ga duk Wanda suke da bukatar hakan.