Kungiyar DOGAA ta shirya taron shan ruwa ga daliban makarantar yan mata ta Dala

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar tsaffin daliban makarantar yan mata ta GGSS Dala (DOGAA) ta shirya taron shan ruwa ga daliban makarantar da adadinsu ya kai dari tara (900) a harabar makarantar .

 

Da take bayani dangane da muhimmancin ciyarwa a Addinin Musulunci musamman a watan Azumin Ramadan, Shugabar kungiya Haj. Saudatu Sani wadda ta samu wakilcin sakatariyar kungiyar ta kasa Haj. Zainab Sule Minjibir, ta ce sun shirya taron shan ruwan ne ga daliban makarantar da malamansu harma da wasu daga Cikin tsaffin Dalibai domin kyautata alaka tsakanin kungiyar da daliban makarantar.

Saudatu Sani ta kuma godewa Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Alh. Tajudeen Aminu Dantata da wasu wakilan Amintattu na kungiyar har ma da wasu daga cikin tsaffin dalibai bisa irin gudunmawar da suka bayar Wajen shirya buda bakin.

A nata bangaren Shugabar kwamitin shirya buda bakin ta kungiyar Haj. Gaji Bello Hussain ta bukaci Alumma su dinga kulawa da taimakawa juna musamman a wannan wata Mai Albarka na Ramadan.

Da dumi-dumi: Kotu Ta Bayyana Shuruddan Bada Belin Murja Kunya

Sannan tayi Kira ga tsaffin Daliban da sukaci gajiyar makarantar Kan cewa su dawo su rika kyautatawa makarantar kamar yadda Suma sukaci gajiya aka kyautata musu.

“Idan Muka kyautatawa daliban nan Muka janyo su jikinmu zasu kasance masu tausayi da kyautatawa inji Haj. Gaji Hussain.”

Mun kashe sama da Naira Miliyan 160 Wajen gyara makarantar G.G.C Dala – Shugabar kungiyar DOGAA

Kazalika Gaji Bello ta ce kungiyar tsofaffin kwalejin Dala ita ce ta kirkiro da Shirin buda bakin la’akari da ladan dake tattare da ciyarwa, tare da cusawa Dalibai akidar dawowa su taimaki makarantar bayan kammala karatunsu.

Zainab Ibrahim da Safiyya Abdullahi na daga cikin daliban da suka kasance a wurin buda bakin, sunce sunci sun sha duk abinda suke bukata yayin Shan ruwan, don haka suna cikin farin ciki sosai Wanda suka dade basuyi irinsa ba.

Karshe kuma sunyi Fatan Alkhairi da addu’a har ma da godiya ga kungiyar DOGAA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...