Daga: Aliyu Danbala Gwarzo
Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwarzo da kabo a zauren majalisar tarayya Abdullahi mu’azu baban gandu ya kaddamar da rabon tallafin kayan abinchi ga mabukata da masu karamin karfi 10,000 a don ragewa al’ummar da yake wakilta radadin matsin rayuwa da suka tsinci kansu ciki.
Hon. Abdullahi muazu yace ” hakika babu lokacin da ya dace mu baiwa al’ummar mu tallafi kamar wannan lokaci da al’umma suke azumin watan Ramadana cikin matsin tattalin arziki”.
“Ya kamata yan siyasa da dukkanin wanda Allah ya hore musu mu tallafawa al’umma Saboda al’ummar suna cikin mawuyacin halin ta yadda wasu ko buda baki basa iya yi Saboda basu da su da abun da zasu yi buɗe bakin”.
Yadda Gwamnatin Kano Ta Ci Gaba Da Rusau Duk Da Umarnin Kotu
Bababan Gandu ya kuma yabawa jagororin su na jam’iyyar APC a yankin musammanministan gidaje da raya burane Eng. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da tshon kwamishinan kananan hukumomin jihar kano Hon. Murtala sule Garo da sauran jagororin bisa goyan bayan da suke bamlsu wajen gudanar da irin wadannan aikace aikace.
Tinubu ya Sauyawa Lawan Jafaru Isa Mukami
Baban Gandu yayi kiraga dukkanin wanda ya rabuta da wanan tagomashi da yayi amfani dashi ta hanyar data dace dubada anbayar da tallafin ne badan komai sai domin ayi amfani dashi ba domin a sayar ba.