Daga Musa Mudi Dawakin Tofa
Sabon Kantoman mulki na Karamar hukumar Dawakin Tofa Dr. Kabiru Ibrahim Danguguwa ya sha alwashin rabawa talakawanta abinci na sama da naira Miliyan goma sha biyar, a lokacin Azumin watan Ramadan.
Kantoman mulkin ya bayyana haka ne yayin da ya jagorancin taron rantsar da mataimakinsa Honarabul Surajo Ahmad Chedi da sakatarensa Nuhu Ibrahim da kuma kansilolinsa 14, a harabar sakatariyar karamar hukumar .
Matsalar Tsaro: Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Baiwa Manyan Jami’an Rundunar Umarni
Dr. Danguguwa ya ce suna sane da halin matsin rayuwa da al’umma ke ciki, a matsayin somin-ta6i, cikin goman farko na watan Azumin Ramadan, kwamitin rikon da yake jagoranta zai raba kayan abinci na sama da naira miliyan goma sha biyar, a mazabu 11 dake karamar hukumar Dawakin Tofa.
Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Sa a Buɗe Iyakokin Najeriya Da Nijar
Dakta Kabiru Ibrahim Danguguwa ya kara da cewa gwamnatinsa zata hidimtawa al’umma matuka da baiwa fannin ilimi fifiko, da inganta fannin lafiya dana tsaro da tsaftar muhalli da kuma bujuro da wasu manufofi da tsare-tsare wandanda zasu inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar Dawakin Tofa .
Ya kuma bukaci yan kwamitin rikon karamar hukumar da su bashi hadin kan da ya dace domin ciyar da karamar hukumar Dawakin Tofa gaba, Sanna ya bukaci suna al’ummar karamar hukumar dasu tallafa musu da addu’o’i don su sami damar sauke nauyin da gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya dora musu.