Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin magance rikice-rikice a matakin farko na jihar kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Shugaban Cibiyar samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice ta Kasa Dr. Joseph Ochogwu ya buƙaci al’ummar jihar Kano da su baiwa kwamitin Magance rikici a Matakin farko na jihar hadin kai don inganta zaman lafiya da ake da shi.

Kadaura24 ta rawaito Dr. Joseph Ochogwu ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan yan kwamitin, wanda cibiyar ta shirya da hadin gwiwar USAID da kwamin zaman lafiya na jihar kano suka shirya a Kano.

Yace a wannan lokaci da Nigeria take fuskantar kalubalen rashin tsaro ta fuskoki daban-daban, akwai bukatar baiwa wancan kwamiti hadin kai domin magance barazanar rashin tsaro tun daga tushe da ake samu a Nigeria .

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Sa a Buɗe Iyakokin Najeriya Da Nijar

“Gwamnatin tarayya ce ta samar da Cibiyar samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice ta Kasa don daukar matakan magance rikice-rikice tun kafin su girma, kuma hakan bazata samu ba har sai al’umma sun bamu hadin kai ta hanyar samar da irin wannan kwamitoci a unguwannisu don magance barazanar da muke fuskanta a Nigeria”. A cewar Dr. Joseph Ochogwu

” Duk girman rikici yana farawa ne daga karami kuma a Cikin al’umma, don haka idan al’umma suka fahimci alamun irin waɗannan rikice-rikice da kuma sanin hanyoyin da za’a shawo kansu, to babu shakka za’a iya cimma nasarori da aka sanya a gaba, kuma a magance matsalolin da ake fuskanta tun kafin su girma “.

Shugaban cibiyar samar da zaman lafiya yayi fatan mahalarta taron zasu fada ilimin da suka samu ta hanyar sanar da yan kwamitin na unguwanni domin magance faruwar rikice-rikice a cikin al’umma da kuma sanin hanyoyin da ake bi wajen sanar da hukumomi abun dake faruwa don su kuma su dauki matakan da suka dace.

Hukumar mu zata farfado da kima da tattalin arzikin Nigeria – Ali Nuhu

 

A nasa jawabin Sakataren babban kwamitin zaman lafiya na jihar kano Amb. Ibrahim Waiya yace yabawa cibiyar samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice ta Kasa da USAID da suka hada hannu wajen shirya taron a jihar kano.

” Muna kira GA daukacin yan kwamitin da suka haɗar da yan sanda, sojojin sama da na kasa, hukumar kula da Gidajen gyaran hali da hukumar Kwastam da hukumar kula da shige da fice ta kasa,DSS da Civil Defense, Hizbah KAROTA da dai sauran su da mai da hankali wajen sauke nauyin da aka dora musu”. A cewar wayya

Yace zasu tabbatar wadanda suka amfana da biyar sun yadata yadda ya dace, sannan ya bada tabbatacin lokaci zuwa lokaci za’a cigaba da shirya irin wannan bitar don cimma nasarori da aka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...