Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kantoman karamar hukumar Gwarzo Dr.Mani TSoho ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don tabbatar da zaman lafiya a karamar hukumar Gwarzo.
Dr.Mani Tsoho ya yi wannan alkawarin ne a lokacin rantsar da mataimakinsa, sakatare da kansilolin karamar hukumar a cibiyar Addinin Musulunci ta Gwarzo .
“Muna fuskantar kwararowar masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami da barayin shanu saboda kusancinmu da jihohin Katsina da Zamfara.” Inji Dr.Mani Tsoho.
Cushe: Hatsaniya ta kaure a Majalisar Dattawan Nigeria
A Cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na shiyyar Gwarzo Rabi’u Khalil ya aikowa kadaura24, yace kantoman ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga dukkan jami’an tsaro da ke aiki a yankin domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A nasa bangaren daraktan kula da ma’aikata na karamar hukumar Ubale Magaji ya taya kwamitin riko a karkashin jagorancin Dr.Mani Tsoho Gwarzo murna tare da godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa zabar yan kwamitin.
Yadda Mace ta Farko da Gwamnan Kano Ya Baiwa Kantoma Ta Sha Alwashi
A nasa jawabin Hakimin Gwarzo Barde Kerarriya Alh. Kabiru Bayero ya yi kira ga mukaddashin shugaban kwamitin rikon da ya kara kaimi kan nasarorin da gwamnatin da ta shude ta samu kan harkokin tsaro.
Alh.Kabiru Bayero yayin da yake taya su murna ya kuma yi alkawarin tallafa wa dukkanin masu rike da sarautun gargajiya da na addini.