Daga Nafisa Abdullahi Bichi
Dan Majalissar tarayya mai wakiltar Bichi kuma Shugaban Kwamitin kasafi na Majalissar tarayya, Hon. Abubakar Kabir Abubakar ya kaddamar da rabon kayan kayan abinchi don tallafawa al’ummarsa sakamakon shigowar azumin watan Ramadan.
An dai fara raba kayan abinchi ne a ranar Lahadin data gabata,inda aka fara da Mazabun Yallami da Kwamarawa duk a Karamar hukumar ta Bichi.
A Cikin wata sanarwa da mai taimakawa dan majalisar kan harkokin yada labarai Jamilu Halliru Master ya fitar, yace Alhaji Kabir Abubakar Kabir dama ya saba raba irin waɗannan kayan abinchi a duk lokaci irin wannan na azumi.
Yadda za ku kula da kanku a lokacin azumin Ramadan
Sanarwar tace ana a bana za’a baiwa magidanta babban buhun shinkafa mai nauyin 50kg, saboda saukakawa al’umma sakamakon halin matsin tattalin arzikin kasa ake fuskanta a bana.
A jawabinsa, shugaban ma’aikatan Ofishin Dan Majalissar Hon. Sabo Iliyasu Saye wanda shi ne ya wakilci dan majalissar yayi kira ga al’ummar da suka rabuta da wannan abinci da suyi amfani da shi yadda ya dace, domin samun nasarar da ta aka raba abinchin.
Yadda Gobara ta tashi a tashar wutar lantarki ta Dan agundi dake Kano
“Dan majalissar tarayyar mu Hon. Abba Bichi a shirye yake ya cigaba da taimakawa al’ummar Karamar Hukumar Bichi yadda ya kamata kamar yadda ya saba”.
” Saboda yanayin da ake ciki Hon. Abba Bichi ya ce a bana kowacce Akwatu da muke da ita a karamar hukumar Bichi za’a baiwa magidanta 100 buhun shinkafa don tallafa musu, a wannan wata mai albarka”.
Taron ya samu halartar daukacin Ma’aikatan Dan Majalissar Tarayya, shugabannin Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Bichi da sauran Al’umma.