Yadda Gobara ta tashi a tashar wutar lantarki ta Dan agundi dake Kano

Date:

Daga Hafsat Yusuf Abubakar

 

Rahotanni da ke fitowa daga Jihar Kano, sun nuna cewar wuta ta kama a tashar raba wutar lantarki da ke Kofar Ɗan Agundi a jihar.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’ummar Musulmi a jihar, ke dakon ganin jinjirin watan azumin Ramadan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gobarar da ta kone manyan injina da taransufoma masu yawa.

Yanzu-Yanzu: An ga Watan Ramadan a Ƙasar Saudiyya

A cewar wani jami’in gudanarwa na Kamfanin Raba Wutar Lantarki a Kano (TCN), ya ce gobarar ta kone manyan taransufoma biyu masu raba wutar lantarki a jihar.

“Ni ma ba na ofis amma sai aka sanar da ni cewa taransufoma biyu sun kone, amma akwai guda daya tana aiki, akwai wata sabuwa wadda har yanzu ba a fara aiki da ita ba.”

Kazalika, jami’in ya ce tashin gobarar ba zai hana raba wuta ba.

Yadda Kalaman Abba Hikima akan Gwamnatin Kano suka tada kura a dandalin sada zumunta

“Wutar ba za ta hana raba wutar lantarki ba tunda guda daya tana aiki. Amma komai zai daidaita yadda ake so da zarar an gyara abubuwan da suka kone.”

Mutanen yankin, sun bayyana cewar ba su san musabbabin tashin wutar ba.

Jin ta bakin kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, ya ci tura zuwa lokacin hada wannan rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...