Daga Usman Hamza
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Engr. Rabiu Kwankwaso zai kaddamar da asibitin kangararru mai zaman kansa, da kuma kula da Masu lalurar damuwa a jihar Kano.
Cibiyar Mai Suna Amana Sanatorium a rikunin Gidaje na jido dake Kano, za a kaddamar da ita a ranar 21 ga Oktoba, 2021, a wani bangare na bikin cika Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Shekaru 65 a Duniya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa kwankwasiyya Kan harkokin kafafen yada labarai Ibrahim Adam ya fitar a ranar Asabar din nan.
Sanarwar ta bayyana cewa Idan za’a iya tunawa a shekarar 2011 lokacin da Sanata Rabiu Kwankwaso ya dawo wa’adi na biyu na Gwamnan Kano, ya gano an Sami l karuwar masu shan miyagun kwayoyi, ‘yan daba da marasa aikin yi.
” Matasa da yawa ‘yan siyasa na amfani da su a matsayin yan barandan siyasa, kuma basu da aikin yi sai jagaliya a ofisoshi gwamnati don neman tsira da rayuwarsu, ” in ji sanarwar.
A cewar sanarwar, wannan ya sa tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Rabiu Kwankwaso, ya kafa kwamitin da zai yi yaki da haramtattun dillalan miyagun kwayoyi da masu shan muggan kwayoyi a jihar Kano a wancan Lokacin.
” Ya kafa cibiyar koyar da harkokin tsaro, duk don rage shan miyagun ƙwayoyi, sece-sace da rashin aikin yi ga matasa marasa ilimi a Kano. ”
” An kafa cibiyar gyara ne don ceto Matasan da suke Shan muggan Kwayoyi domin su zamo Masu amfanar kansu da Kuma al’umma, Sannan Kuma a rage yawan laifuffuka a Kano.
Веном 2 – смотреть онлайн в хорошем качестве https://bit.ly/venom2-2021