Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Babbar kotun jihar Kano mai Lamba 5 dake zamanta a sakatariyar Audu Bako ta haramta sanya wakokin Chass da Asosa na mawaki Ado Gwanja.
Da take zartar da hukunci mai shari’a Aisha Ibrahim Mahmud ta bayar da umarni haramta sanya wakokin a dukkan taruka na jama’a har zuwa lokacin da hukumar tace Fina-finai zata kammala tantancesu.
Cikakken Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Haramtawa Ado Gwanja Yin Waƙa, Bayan Kama Shi
Umarnin na kunshe ne cikin wata takarar Kara mai lamba k/m/383/2023, Inda a ciki takardar mai Shari’a Aisha Mahmoud ta ce ta kori karar da ado Gwanja ya shiga yana kalubalen ta wata kotun Shari’ar Musulunci dake Bichi da cigaba da sauraron karar da zauren malaman kano suka shigar akan sa.
Yan Sanda Sun Kama mutane 9 Masu Chanjin kudaden Waje ba Bisa ka’ida ba
Tun da farko dai Ado Gwanja ne ya shiga da karar a gaban babbar kotun jihar kano yana Kalubalantar Umarnin da kotun Shari’ar Musulunci dake Bichi ta bayan na a kamo shi.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a jiya litinin kotun ta bada umarnin a kamo mawaki ado Gwanja tare kuma da Haramtawa mawakin sake yin waka har sai kammala bincike kan Shari’ar da zauren malaman jihar kano suka kai shi, sakamakon yin wata waƙa mai suna WAR.