Kungiyar Masu Gidajen Burodi ta Tsunduma Yajin Aiki a Nigeria

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukanta daga yau talata 27 ga watan Fabarairu, 2024.

Kadaura24 ta hakan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mansur Umar, ya sawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai.

Idan Muka Cigaba da Hakuri Al’ummar Nigeria Da Yawa ne Zasu Mutu – Shugaban Yan Kwadago

ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan matsayar ce bayan kammala wani taron gaggawa na musamman da ta kira domin matsa wa gwamnati lamba kan ta ɗauki matakin sauƙaƙa kasuwancin masu sarrafa fulawa a Nigeria.

Sanarwar ta ce duk wasu ayyukan haɗawa ko sayar da burodi ya kawo ƙarshe ne a jiya Litinin, 26 ga wata, kuma yajin aikin zai ci gaba har nan da mako ɗaya.

Yan Sanda Sun Kama mutane 9 Masu Chanjin kudaden Waje ba Bisa ka’ida ba

Wannan dai zai ƙara dagula lamurra a ƙasar, daidai lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar – NLC ta kira zanga-zanga ta gama-gari.

Najeriya dai na fama da tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ya kai ga masu kamfanoni ƙara farashin kayan da suke samarwa sanadiyyar hauhuwar farashin kayan da suke amfani da su.

Fulawa na ɗaya daga cikin kayan masarufi da farashinsu ya yi tashin gwauron-zabi tun bayan da ƙasar ta shiga cikin halin tangal-tangal na tattalin arziƙi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...