Daga Halima Musa Sabaru
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane 9 da ake zargin yin Kasuwanci hadadar kudaden kasashen waje ba bisa ka’ida ba a Kano.
Kadaura24 ta ruwaito cewa hadakar jami’an tsaro karkashin jagorancin rundunar ‘yan sandan Kano da suka hada da jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC da kuma hukumar kwastam ta Najeriya a ranar 21 ga watan Fabrairun 2024 da misalin karfe 1100 na safe ne suka kai samamen.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce an gudanar da aikin ne kamar yadda doka ta tanada a wadannan wurare kamar haka: (1) Kasuwar yan chanji ta Wappa dake karamar hukumar Fagge (2) Bayan ofishin CBN karamar hukumar Nassarawa (3) Central Hotel, Bompai Road, a karamar hukumar Nassarawa (4) Ashton Road, (5) Mallam Aminu Kano International Airport (MAKIA), (6)Tashar Kofar Ruwa dake karamar hukumar Dala (7) Kasuwar hatsi ta Dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa.
Cikakken Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Haramtawa Ado Gwanja Yin Waƙa, Bayan Kama Shi
Sanarwar ta kara da cewa, ”A karshen samamen, an kama mutane talatin da daya (31) daga cikin su ashirin da biyu (22) an tantance basu da wani laifi, yayin da kuma ake zargin Tara (9) daga cikin su, sakamakon wasu abubuwa da aka same su da su ; (1) Dalar Amurka talatin da takwas ($38:00), (2) Dari daya da sha uku na shaifa (CFA 113:00) Kudin Nijar, (3) Dubu Hudu Dari Takwas da Goma (Cairo 4,810:00) Fam din kasar Masari, (4) Dari Biyu (Birr 200:00) Kuɗin Habasha, (5) Na’urar POS ɗaya (1), da Na’urorin Wayar Hannu biyu (Infinix Android & Techno Keypad) guda (6).
Sanarwar tace za’a gurfanar da wadanda ake zargin su tara (9) a gaban kotu mai lamba 70 Normandsland Kano .
Manufar kai samamen ita ce domin tsaftace kasuwar hadadar kudaden kasashen waje daga bata gari, “in ji sanarwar.
”Kwamishanan ‘yan sanda, CP Mohammed Usaini Gumel, ya yabawa jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, da hukumar kwastam ta Najeriya bisa jajircewa, hadin kai wajen ganin an samu nasarar aikin .
CP ya kuma shawarci mutanen da masu gudanar da hada-hadar kudaden kasashen waje, da su yi Kasuwancinsu kamar yadda doka ta basu dama, kuma su sami lasisin fara Sana’ar kuma koyaushe su guji ayyukan da ba su da kyau. CP ya kuma jaddada cewa, tare, za mu iya samar da tsarin kudi na gaskiya da rikon amana ga dukkan mazauna jihar Kano.