Kungiyar Kwadago ta bayyana matakin da zata dauka idan aka kaiwa ya’yanta hari yayin zanga-zanga

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nigeria (NLC) ta ce ta na da masaniyar cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki sojojin-hayar wasu zauna-gari-banza domin su kai wa mambobinta hari idan suka fita zanga-zanga a ranar Talata da Laraba.

NLC ta tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa idan aka kuskura wasu zauna-gari-banza suka afka wa masu zanga-zanga, to za su bada umarnin gaba ɗaya kowa ya tafi yajin aiki, komai ya tsaya cak, tattalin arzikin ƙasa shi ma ya yi tsayuwar-gwamin-jaki.

“Idan aka kai mana hari, to komai zai tsaya cak a ƙasar nan. Ma’aikata za su daina zuwa aiki. Kada ma a yaudari kowa, mu da sauran ‘yan Najeriya da aka gasa wa raɗaɗin tsadar rayuwa fa ba wanda ya isa ya yi mana wata barazana,” cewar Shugaban NLC, Joe Ajaero, cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.

Zanga-Zangar NLC: Kungiyar Yarbawa Ta Baiwa Yan Kabilar Umarni

Ajaero ya bayyana sunan gungun wasu da ya kira ‘yan ta-kifen da gwamnatin tarayya ta kafa cikin gaggawa, ta ke kashe masu kuɗi domin kawai su hargitsa waɗanda za su fita zanga-zangar lumana a ranakun Talata da Laraba. Za su fita zanga-zangar nan saboda yunwar da aka ƙaƙaba mana.”

Za Mu Fara Daukar Mataki Akan Masu Yin Gine-Gine ba Tare da Neman Iziniba a Kano -KNUPDA

Kungiyar Kwadagon dai ta shirya fita zanga-zangar lumana a ranakun Talata da Laraba, wato 27 da 28 ga Fabrairu, saboda raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan.

Gwamnatin Tarayya dai na ta roƙon NLC kada su tafi yajin aiki, domin a cewar ta, ta na bakin ƙoƙarin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da shi ne.

Amma a ranar Lahadi Shugaban NLC ya ce ba gudu ba ja da baya, za su yi zanga-zangar lumana a ranakun Talata da Laraba. “Kuma ba a magance yunwa ko matsalar tattalin arzikin ƙasa ta hanyar dankwafe masu zanga-zangar lumana.” Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...