Yan Magani: Rundunar Yan sandan Kano ta Bayyana Dalilan kama mutane 3

Date:

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku kan yunkurin tada hargitsi sakamakon rufe shagunan ‘yan magani da ke kasuwar Sabon Gari a jihar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hussaini Gumel ne, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), a ranar Lahadi a jihar.

Gumel, ya ce lamarin ya faru ne daidai lokacin da wasu ’yan kasuwar ke kwashe kayayyakinsu zuwa sabuwar kasuwar Kano Economic City, da ke dangwauro, a wajen birnin.

Zanga-Zangar NLC: Kungiyar Yarbawa Ta Baiwa Yan Kabilar Umarni

Ya bayyana cewa wasu bata-gari sun yi yunkurin haifar da hargitsi a wurin, amma ba tare da bata lokaci ba ’yan sanda suka tarwatsa su.

A cewarsa, manufar wadanda ake zargin shi ne kutsawa cikin shagunan mutane domin satar kayayyaki.

Kwamishinan, ya ce wadanda ake zargin yanzu haka suna hannun ’yan sanda, inda ya kara da cewar sun bai wa ’yan kasuwar tsaro don kwashe kayansu cikin salama.

Ya ce an tura karin jami’an ’yan sanda kasuwar don bai wa ‘yan kasuwar damar kwashe kayansu cikin sauki da tsaro.

ECOWAS ta Bayyana Dalilan da Suka sa Ta Janyewa Nijar, Mali da Burkina Faso Takunkumi

Idan ba a manta ba gwamnatin Kano, ta bayar da umarnin rufe shagunan masu sayar da magunguna a kasuwar Sabon Gari, lamarin da ya haifar da cece-kuce a jihar.

Wasu na ganin ba a yi ’yan maganin adalci ba.

A gefe guda kuwa, gwamnatin Kano ta bayyana cewar akasarin masu sayar da maganin da ke kasuwar ba sa kan ka’ida duba da dokokin da ke tattare da harkar sayar da magunguna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...