ECOWAS ta Bayyana Dalilan da Suka sa Ta Janyewa Nijar, Mali da Burkina Faso Takunkumi

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta ce matakin dage takunkumin da aka kakabawa kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso ya samo asali ne kan bukatar tabbatar da hadin kai da tsaro a yankin.

Dr Omar Touray, shugaban hukumar ta ECOWAS ne ya bayyana haka a karshen wani zama na musamman da shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka yi ranar Asabar a Abuja.

Ya ce hukumar ta lura da karatowar lokutan Azumin watan Ramadan da kuma tasirinsa ga al’ummar wadancan kasashe, sannan kuma da yadda manyan shugabanni da kamar su Janar Yakubu Gowon mai ritaya suka sanya baki.

“Hukumar ta yi la’akari da cewa janye takunkumin zai yi tasiri a siyasance, zamantakewa da tattalin arziki, ga hukumomin kasashen uku da kuma ECOWAS a matsayin yanki.

Kamata yayi Gwamnati ta cirewa kayan masarufi haraji ta mai dashi kan Giya, sigari da kayan kyalekyale – Falakin Shinkafi

“Hukumar ta tuna cewa, a cikin tsarin hadin gwiwar yankin na yaki da ta’addanci, tsatsauran ra’ayi da muggan laifuka, kasashen uku sun amfana da kusan dalar Amurka miliyan 100 da UMR ta tara a cikin tsarin shirin ECOWAS na yaki da ta’addanci.

“Bugu da kari kuma, an ware wasu kudade, kimanin dalar Amurka miliyan 7.5 ne ake badawa domin tallafawa kasashen uku wajen samun kayan aikin da zasu taimaka wajen yaki da ta’addanci.

“Janyewar zai shafi hadin gwiwar tsaro ta fuskar musayar bayanan sirri da kuma shiga cikin shirye-shiryen yaki da ta’addanci a yankin.

Touray ya kara da cewa ficewar kasashen daga cikin kungiyar zai sa su zama saniyar ware a fannin diflomasiyya da siyasa a fage na kasa da kasa, inda yan takarsu da zasu nemi wani matsayin na kasa da kasa baza su sami goyon baya ba.

Tinubu ta gargaɗi Kungiyar Kwadago kan zanga-zangar da ta shirya yi a Nigeria

“Hukumar ta fahimci cewa janyewar za ta yi tasiri kai tsaye kan yanayin shige da fice na ‘yan kasar, saboda ana iya bukatar su da sai sun yi takardar bizar tafiye-tafiye kafin shiga wata kasa a yankin.

Kasashen uku za su daina amfani da fasfo na ECOWAS a duk fadin yankin, da kuma daina cin moriyar inshorar motocin kati mai launin ruwan kasa.

“Hukumar ta amince da cewa Kasashen uku na wakiltar kashi 17.4 na al’ummar yankin sama da miliyan 425.

Duk da cewa suna wakiltar kashi 10 cikin 100 na GDP na yankin, ficewarsu zai rage girman kungiyar ta ECOWAS.

Ya ce an dage takunkumin ne don inganta kasuwanci da fa’idojin da aka samu daga ayyuka da shirye-shirye da dama na yankin da suka hada da tanadin abinci na yankin.

“Shirin tallafa wa makiyaya masu karfi a yankin Sahel, wanda bankin duniya ke ba da tallafin kudi dalar Amurka miliyan 215, shi ma wani aiki ne da ya amfanar da kasashen uku.

“Kasashen ukun kuma sun ci gajiyar shirin tallafin noman rani na yankin Sahel, wanda bankin duniya ke ba da tallafin kudi har dalar Amurka miliyan 103.

“Tsarin tallafin abinci na Kasashen guda uku ya kai dala miliyan 230, wanda Bankin Duniya ya bayar, kuma yana amfanar kasashen uku.

Ya ce sauran ayyukan da kasashen ke amfana da su sun hada da harkar wutar lantarki ta yankin ECOWAS, aikin Pool na Afirka ta Yamma, wanda ya hada kasashe mambobin kungiyar da cibiyar samar da wutar lantarki a yankin domin inganta wutar lantarki.

Ya ce rashin dage takunkumin zai haifar da dakatarwa da duk wasu ayyuka da shirye-shiryen ECOWAS na sama da dalar Amurka miliyan 500.

Touray ya ce, ayyukan da aka yi gaba daya sun kai kusan dalar Amurka miliyan 321.6.

“Bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a matakin hukumomi, hukumar ta lura cewa janyewar ba wai kawai yana buƙatar rufe wasu yankuna hudu a Burkina Faso ba, hukumomin yanki biyu a Mali da kuma ofishin yanki daya a Asiya.

“Hakan kuma zai shafi tsaron ayyukan ECOWAS kusan 130 wadanda a halin yanzu ma’aikata 77 sun fito ne daga Burkina Faso, 23 kuma sun fito daga Mali, sai kuma 32 daga Nijar. (NAN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...