Da dumi-dumi: Bayan Zanga-Zangar Masu Shara a Kano, Danzago ya koka

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Wasu masu sharar tituna a birnin Kano, sun yi zanga-zangar kin amincewa da matakin da hukumar kula da tsaftar muhalli ta kasa (REMASAB) ta dauka na kin biyansu albashi na watanni 10 da suka gabata.

Majiyar kadaura24 ta Daily News24 ta rawaito masu shara a tituna sun hallara a hedikwatar hukumar ta REMASAB a ranar Talata inda suka yi kira ga manajan daraktan hukumar Alhaji Ahmad Danzago da ya biya su albashi.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa duk da hadarin da aikinsu yake da shi, da kuma yadda aka kashe wasu daga cikinsu a yayin da suke bakin aiki a wurare daban-daban a cikin birnin Kano, amma har yanzu hukumar ta gaza biyansu hakkokinsu.

Zanga-zanga: Kungiyar Kwadago ta yiwa Hukumar DSS Martani

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da sun yi magana bisa sharadin boye sunansu sun ce sun boye Sunayen su don fargabar fuskantar cin zarafi daga hukumar REMASAB.

“Muna rokon Gwamna (Abba Kabir Yusuf) da Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da su sanya baki don a magance wannan matsalar, kuma su tabbatar an biya mu albashin mu.

Ya kara da cewa “Muna kasada rayukanmu domin tsaftace jihar, sannan kuma mun yi asarar rayuka da dama a cikin wadanda muke sharewa a cikin jihar.”

Sai dai da yake mayar da martani shugaban Hukumar kwashe shara da tsaftar muhall ta jihar kano ya yi Allah Wadai da yadda wasu marasa kishin jihar kano suke daukar nauyi tare da tunzura wadanda basu ji ba basu gani ba domin su yiwa hukumar zanga-zangar bata suna akan rashin biyan su hakkin su.

Shugaban Hukumar na jihar kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago, shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Yadda wasu Matasa suka daka wa motocin Abinchi wawa a jihar Neja

A cewar Dan zago har yanzu bai wuce watanni bakwai da fara Shugabancin hukumar ba, Kuma da zuwan sa ya tantance halattattun ma’aikata tare da biyan su bashin albashin su na watanni 4.

Dan Zago daga nan sai ya bayyana cewa hukumarsa a shirye take wajen daukar dukkan matakan da suka kamata domin dakile wadanda suke kokarin batawa hukumar da gwamnatin jihar kano suna ta hanyar siyasantar da aikin gwamnati.

A baya-bayan nan ne dai wasu da suka kira ka. Su da ma’aikatan hukumar suke ta gudanar da zanga-zangar lumana a ofishin hukumar inda suke zargin shugaban Hukumar da cinye musu hakkokin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...