Zuwa ga
Maigirma Hon. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Audu Bako Secretariat, Kano.
Ranka ya daɗe
BUKATAR DUBA NA TSANAKE BISA KUDURI DA AKA TURO MAJALISA NA A RUSHE MASARAUTUN JIHAR KANO DOMIN SAMUN YANAYIN ZAMAN LAFIYA WANDA SHI YAFI DACEWA A JIHAR KANO.
Cibiyar Kiraye-Kiraye da Samar da Cigaba, ba kungiyar gwamnati bace, ba ta kabilanci bace, ba kuma don kasuwanci aka ƙirƙireta ba, ba kuma don nuna ɓangaraci na addini ba, kungiya ce mai zaman kanta, wadda aka kafa ta a shekarar 2008, don sadaukar da bada gudummawa don samun dorewar dimokuradiyya. inda muke iya ƙoƙari wajen ganin mun magance kalubalen dimokuradiyya, wariyar jinsi, cin zarafin jinsi, kiwon lafiya, muhalli, inganta zaman lafiya da shugabanci na gari.
Munyi imani da jajircewarmu da yakinin cewa samar da al’umma ta gari abu ne mai yiwuwa, amma kuma baza a iya samun cigaba mai dorewa ba sai ta hanyar hadin gwiwa na gwamnatocin jihohi da wadanda ba iya na jiha ba, mun tsaya tsayin daka wajen yin la’akari da kimarmu a duk abin da muke yi.
Maigirma Shugaban majalisa, mu kungiya ce dake wakiltar muryoyin kungiyoyin farar hula da malamai, masu gwagwarmayar samar da kyakkyawar dimokuradiyya da masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Arewa da Najeriya baki daya. Muna aiki daidai a jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Don haka muna rubuto wannan wasiƙa don nuna damuwar mu saboda mun damu matuƙa da cigaban jihar kano inda muka samu labari kan wani kira da wata kungiya tayi na a rushe sabbin masarautun da tsohuwar gwamnatin jihar Kano Karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro a Kano, wani lokaci a shekarar 2019. Bari in tunatar da kai Mai girma cewa, dukkan Jihohin Arewacin Nijeriya suna da alaka da Jihar Kano, kai tsaye ko a fakaice, don haka duk shawarar da za a yi ta fannin zamantakewa, tattalin arziki da siyasa a Jihar Kano, na da dabi’ar yin tasiri ga mazauna wasu jihohin au imma zaman lafiya ko akasin haka. Don haka ne ya sa dukkan mazauna Arewacin Najeriya na da hakkin fadin albarkacin bakinsu game da abubuwan dake faruwa a jihar Kano, ta hanyar bayyana ra’ayoyinsu da nufin taimakawa wajen bada shawarwarin da za su taimaka wajen cimma matsaya ta hankali cikin hikima.
Batun ajiye aikin Sheikh Daurawa, Hisbah ta Magantu
A kan wannan batu, muna so muyi amfani da wannan damar don jawo hankalin ku game da abubuwan dake tattare da mayar da martani ga zanga-zangar neman Majalisar Dokoki, don ruguje sabbin masarautun jihar kano. Domin kuwa, yanayin bai ma dace a yi la’akari da irin wannan mataki ba, lokaci bai yi ba, don kuwa shawarar tana bukatar tunani da hankali, don duk domin a kaucewa cigaba rushe daraja da sauran martaba da jihar kano keda ita a idon duniya, da kuma dakatar da ƙiyayyar da tsohuwar gwamnatin jihar Kano Karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje tayi a tsakanin al’ummar Jihar Kano da masarautun ta.
Maigirma Shugaban majalisa, bari mu sanya wannan a rubuce cewa bamu taba goyon bayan abinda tsohuwar gwamnatin kano tayi ba, kasancewar rage daraja ne ƙiri-ƙiri amma haka aka rufe ido aka aiŵatar da abunda bai dace ba. A saboda haka muke kira da wannan majalisa da tayi duba na tsanake kuma cikin hikima da tunani mai kyau irin na dattawa kafin ace an ɗauki mataki wanda zai jefa jihar kano cikin wani yanayi da ba’a fata.
Yallabai, wannan wasikar tamu tana dauke ne da irin soyayyar da muke yiwa jihar Kano, da jama’ar dake cikin ta tare da kaskantar da kai ga majalisa, muna kuma jawo hankalin da kada a tafka wannan kuskuren wanda muke ganin ba zai haifar da ɗa mai ido ba. wanda kuma hakan ka iya janyoea da a rubuta sunan ka da baƙin alƙalami kamar yadda aka rubuta na Dakta Abdullahi Umar Ganduje da baƙin alƙalami.
Ba a dade ba jihar Kano ta samu kanta daga cikin rudanin dake tafe da rikicin siyasa, don haka baza mu iya yin amfani da kudinmu wajen gayyato wata matsalar wadda zata illata mu ba. Wajibi ne ’yan kasa marasa laifi su zauna lafiya.
Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano Ya Magantu Kan Sakin Murja Kunya Daga Kurkuku
Mun kuma yi imanin cewa, kuma kuna sane da irin wahalhalun da ’yan Najeriya ke ciki, kada mu bari ayi amfani damu wajen haifar da wata matsala da zata iya kawar da kwanciyar hankali da mazauna yankin kano ke samu.
Naka
Ibrahim Yusuf, Babban Darakta na cibiyar Kiraye-Kiraye da samar da Cigaba.