Batun ajiye aikin Sheikh Daurawa, Hisbah ta Magantu

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ake yadawa na cewa kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayi murabus .

Mataimakin Kwamandan Hukumar, DCG, Dr. Mujahid Aminundeen, ne ya karyata rahotannin ta cikin wani sakon murya da ya aikawa jaridar Daily News24.

Tun da farko dai an yi ta yadawa a kafafen sada zumunta cewa Sheikh Daurawa ya ajiye aikinsa, sakamakon yadda aka saki Murja Ibrahim kunya bayan hukumar Hisbah ta kamata tare da gurfanar da ita a gaban kotu .

Kotun da ke Shari’ar Murja Kunya ta Bayyana Dalilan Fitar da ita Daga Gidan Yari

A cikin faifan sautin, DCG Aminundeen, ya ce, “Ina son nanata wa al’ummarmu cewa, Al-Sheikh, Al-Imam, Aminu Ibrahim Daurawa har yanzu shi ne Babban Kwamandan Hukumar Hisbah. Bai yi murabus ba. Har yanzu yana kan kujerar da, Wataƙila, wasu suna so su yi amfani da jita-jita don yin wani abu da bai dace ba, to muna kara jaddada cewa har yanzu yana kan mukaminsa kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa.”

An tattauna yadda za’a samar da sauki yayin aure a karamar hukumar Bagwai

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne dai ya sake nada Shahararren Malamin addinin Islama a matsayin Kwamandan Hukumar Hisbah ta Kano.

Daurawa ne ke jagorantar hukumar a karo na uku, inda a baya ya yi wa’adi biyu a karkashin tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma wa’adin farko na Abdullahi Umar Ganduje.

A shekarar 2018 ne ya sanar da murabus dinsa sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin tsaffin gwamnonin biyu, Kwankwaso da Ganduje.

Ana dai kallon shugaban na Hisbah a matsayin wanda ya taka rawar gani wajen nasarar jam’iyyar NNPP a zabukan da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...