Daga Rahama Umar Kwaru
Mai magana da yawun manyan kotunan shari’ar addinin musulinci na jahar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya bayyana cewa lauyoyin gwamnatin jihar Kano masu gabatar da Kara ne suka karɓi Murja Ibrahim kunya daga gidan yari domin cigaba da bincike.
“Rade-radin da ake ta yi na cewar tauraruwar TikTok Murja Kunya, an sake ta ko an bada ita beli , yace magana ta gaskiya Murja, ta na waje tun ranar Alhamis din data gabata”.
Mizammil Ado Fagge ya ce sun tuntubi kotun da ake yin shari’ar, inda ta shaida mu su cewa lauyoyin ma su gabatar da kara ne, suka zo suka ari Murja , domin ci gaba da tuntubarta kan wani zargi da ake yi mata.
Hukumar Gidan Gyaran Hali ta Kano ta Magantu Kan Bacewar Murjar Kunya a Gidan Yari
” Amma ba abun mamaki ba ne dan an bayar da belin Murja Kunya, saboda na farko wannan laifi da ta yi ba laifi ba ne wanda za a ki bayar da ita belin ta” a cewar Muzammil Fagge”.
Ya kara da cewa, Hurimin kotu ne ta bada beli ko ta hana, amma dai magana ta gaskiya Murja ba ta gidan gyaran hali tun ranar Alhamis din data gabata.
”Wannan ba sabon abu ba ne, sai dai kawai ita saboda labarin ya ya mutsa hazo kuma ga abubuwan da ta ke yi , wanda ya saba da al’ada da kuma addinin mu na Musulinci shi yasa mutane kowa hankalina ya koma kai”.
Idan za’a iya tunawa kadaura24, ta rawaito hukumar kula da gidan gyara hali ta kasa reshen jihar kano ta bayyana cewa tun ranar Alhamis ta saki Murja bisa umarnin kotu.
Tun a daren jiya dai ake ta rade-radin an nemi Jarumar TikTok din Murja Ibrahim kunya a gidan gyaran hali an rasa ta, wanda hakan tasa Ake zantuka da korafe-korafe akai musamman a dandalin sada zumunta.
Ko a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, aka fara gurfanar da ita, bisa yada kalaman batsa da rashin tarbiya, har a wancan lokacin aka yanke mata hukuncin yin shara, a Asibitin Murtala Muhammed dake kwaryar birnin Kano.
Sai dai al’umma na ganin aiyukan rashin da’ar da Murja Kunya ke yi, kara yawa suke yi, shi yasa ma hukumar hisbar ta kamo ta, don tauna aya dan tsakuwa taji tsoro.
Yanzu kallo ya koma sama ga kotun shari’ar addinin musulincin kan hukuncin da zata yanke wa Murja Kunya, idan ta same ta da laifi, da kuma kalubalen da ke gaban hukumar hisbar bisa, zargin tsoma bakin wasu yan siyasa kan sakin Murja Kunya